Na Fasa Auren: Budurwa Ta Saka Zoben Baikonta a Kasuwa, Zata Siyar N8m

Na Fasa Auren: Budurwa Ta Saka Zoben Baikonta a Kasuwa, Zata Siyar N8m

  • Wata matashiyar budurwa ta saka zoben baikonta a kasuwa bayan ta soke aurenta da habibinta
  • Farashin zoben ya kai naira miliyan 10.2 kuma ta dage sai a yanar gizo zata sayar da shi tunda dai an soke auren
  • Wasu da dama sun shawarceta da ta mayarwa saurayin da zobensa cewa siyar dashi sam ba daidai bane

Wata matashiyar budurwa da ta soke aurenta ta saka zoben baikonta da farashin shi ya kai naira miliyan 10.2 a kasuwa.

Bayan ya bayyana karara ba yin auren za a yi ba, sai ta garzaya shafin Facebook domin tallata tsadadden zabon sumfurin Tifanny.

Budurwa da zobe
Na Fasa Auren: Budurwa Ta Saka Zaben Baikonta a Kasuwa, Zata siyar N8m Hoto: High End/Facebook and Tommaso79/Getty Images.
Asali: UGC

Ta saka farashin zoben na lu’u-lu’u kan $18,500, wanda yayi daidai da naira miliyan 8 wanda yayi kasa da farashin yadda aka siye shi.

Matar yar kasar Australiya ta saka zoben na dan wani lokaci, wanda hakan na iya zama dalilinta na rage farashin.

Kara karanta wannan

Duk ‘Dan Da Yace Uwarsa Ba Za Ta Yi Bacci Ba: Uwa Ta Goya Diyarta A Bayan Mutum-mutumi, Bidiyon Ya Kayatar

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ina yi, yanzu bana yi, cewarta

Da take tallata zoben a Facebook, matar tace za ta siyar da hadadden zoben ne saboda wasu dalilai da ke a bayyane.
“Zan siyar da wannan sabida dalilai da suke a bayyane, ina yi, yanzu bana yi.”
“Sabanin yadda farashin zoben Tiffany yake kan $23,600 kowani karat 1.0, zan bar wannan hadadden kan $18,500. Yanayinsa kusan sabo ne – ba a saka shi sosai ba.
“Ayi hakuri babu risit domin bani na siye shi ba. Biyan kudi ta banki kawai."

Jama’a sun yi martani

Wasu mutane sun bukaci da ta gaggauta mayarwa mai zobe da zobensa tunda dai an soke bikin nasu kuma bata da hurumin aikata abun da take shirin yi.

Wasu kuma sun ce zobenta ne tunda tamkar kyauta ne daga mutumin.

Sun ce sam babu laifi don ta siyar da abun da aka bata a matsayin kyauta.

Kara karanta wannan

Da Sauran Aiki: Sanatar PDP Ta Gano Katuwar Matsala a Cikin Kasafin Kudin 2023

Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Kyakkyawar Budurwa Karo Na 3 Cikin Makonni

A wani labarin kuma, jama’a na ta cece-kuce a shafukan soshiyal midiya kan aure-auren da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ke yi a baya-bayan nan.

Yan makonni bayan ya auri matarsa ta biyu, attajira Mariam Ajibola Anako, babban basaraken kasar yarbawan ya sake auren mata ta uku mai suna, Tobi Phillips.

An gudanar da bikin auren wanda ya samu halartan makusanta a ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel