Matashi Ya Sheke Mahaifinsa Har Lahira Bayan Ya Rafka Maka Itace

Matashi Ya Sheke Mahaifinsa Har Lahira Bayan Ya Rafka Maka Itace

  • Wani matashi ya halaka mahaifinsa a yankin Issele-Uku da ke karamar hukumar Aniocha ta arewa a jihar Delta
  • Rigima ta kaure a tsakaninsu ne bayan uban ya zargin dan nasa da girbe masa amfanin gona ba tare da izininsa ba
  • Yaron ya ce ya yi amfani da itace ne wajen rafke mahaifin nasa yayin da ya yi kokarin saran shi da adda

Delta - Wani matashi mai shekaru 25 mai suna Kido, a garin Issele-Uku da ke karamar hukumar Aniocha ta arewa, jihar Delta, ya halaka mahaifinsa.

Wanda abun ya ritsa da shi mai suna Mista Ikechukwu Onyegai, ya mutu ne bayan fada ya kaure tsakaninsa da dan nasa wanda ya zarga da girbe albarkatun gonarsa ba tare da izininsa ba, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Ita Ta Nemeni Da Soyayya": Dan Jarida Makaho Yayi Tsokaci Kan Aure da rayuwarsa

Yan sanda
Matashi Ya Sheke Mahaifinsa Har Lahira Bayan Ya Rafka Maka Itace Hoto: Premium Times
Asali: UGC

An tattaro cewa marigayin ya yi gaba-da-gaba da dan nasa a gonarsa a ranar Juma’a sannan al’ummar yankin Ykpai sun kama mai laifin inda suka mika shi ga yan sanda.

Da yake tona abun da ya faru, wanda ake zargin ya ce rikici ya fara ne lokacin da mahaifinsa ya yi yunkurin daukar addansa sannan ya rafke shi da icce.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce:

“Ya zo ya same ni a gonar inda nake aiki, sannan yayi kokarin kwace addan saboda babu jituwa a tsakaninmu. Da ya daga adan sannan yayi barazanar yanka ni, sai na kare shi da icce sannan nayi amfani da itace na rafke shi.
“Yayin da yake kaiwa kasa, wayarsa ta fado daga aljihunsa, sannan na karne kayar. Ban san cewa zai mutu ba. Itace nayi amfani da shi.
“Lokaci da nake tafiya gona, kowa ya ganni. Ban dauki komai ba.”

Kara karanta wannan

Matashi Mara Kafafu da Hannaye Yana Sarrafa TikTok a Bidiyo da Lebensa, Ya Ba Jama’a Mamaki

Kakakin yan sandan jihar Delta, DSP Edafe Bright, ya tabbatar da faruwar lamarin, Daily Trust ta rahoto.

Mai wankin mota ya ragargaza Benz GLC da aka kawo masa wanki bayan ya ari motar zuwa siyan abinci

A wani labari na daban, mun ji cewa wani dan Najeriya mai wankin mota ya fada cikin matsala bayan ya tuka motar da aka kawo masa wanki zuwa wajen siyan teba da miya sannan ya yi kaca-kaca da motar.

A cikin bidiyon da @drive234 ya wallafa a TikTok, an ga mai wankin motar yana duke kan gwiwowinsa tare da rokon mai motar da ya gafarta masa.

Motar ta lalace sosai kuma saurayin ya yi nadama amma bidiyon bai nuno ko an yafe masa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel