Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aikin ASUU Yau

Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aikin ASUU Yau

  • Gwamnatin tarayya dai ta shigar da Ƙungiyar ASUU kara ne dan neman ƙungiyar komawa bakin aiki
  • Kotun Ma'aikata NIC ta umurci Malaman ASUU su koma aji bayan watanni bakwai suna yaji
  • Suma dai Ƙungiyar sun daukaka ƙara ganin gwamnatin da kotu basu yi musu adalci ba

Kotun daukaka kara mai zamanta a Abuja, ta sanya yau Juma'a dan yanke hukuncin game da ƙarar da ASUU ta shigar na ƙin amincewa da hukuncin da kotun masana'antu ta yanke.

A ranar 21 ga watan Satumba ne babbar kotun masana’antu ta ba da umarnin Ƙungiyar da su koma bakin aiki kafin warware takaddamar da ke tsakaninsu da gwamnatin tarayya.

Ba mu gamsu da hukuncin da karamar kotu ta bayar ba, hakan nafitowa ne ta bakin lauyan Ƙunyar ASUU Mista Femi Falana SAN, shine muma muka shigar da ƙara dan ƙalubalantar gwamnati da nuna rashin dacewar kotun ƙasa wajen saurarar ƙara

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani Ta Koka Kan Yadda Ake Cigaba da Yi Musu Kisan Gilla

Falana ya yi ikirarin cewa

"Yana da ga cikin haƙƙin wanda ake ƙara, shigarwa ko ɗaukaka ƙara muddi hukuncin da akai masa bai mai sa ba"
"yana da ga cikin abinda muka bi wajen tabbatar da ɗaukaka ƙara dan ganin mun kwatowa ASUU hakkinta"

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

ASUU.
Kotun Daukaka Kara Za Ta Yanke Hukunci Kan Yajin Aikin ASUU Yau
Asali: Twitter

Babban Lauyan wanda ya shedawa Mai shari'a Hamma Barka wanda ke cikin mutum Ukun da ke saurarar ƙara, kan suyi watsi da ƙarar ko tuhumar da gwamnatin ke yiwa ASUU, sannan kuma a tabbatarwa da ƙungiyar damarta na daukaka ƙara.

Lauyan yana mai ƙara nusantar da Mashar'anta kan irin tanadin dokoki da tsarin shari'a da ASUU ke da shi kan gwamnatin tarayya.

Yayin da Lauyan gwamnati ke maida suka kan bayanan da Falana Yayi, Igwe ya bayyyanawa kotu rashin dacewar saurarar karar Ƙungiyar tare da tabbatar da cewa kungiyar bama ta bi ƙa'idoji ba wajen ɗaukaka karar.

Daga Ƙarshe dai alkalin kotun ya sanar da Yau, 7 ga watan Oktoban wannan shekarar a matsayin ranar yanke hukunchi, rahoton Leadership.

Asali: Legit.ng

Online view pixel