Bambarakwai: ‘Dan APC Ya Ki Amsar Mukamin da Aka Ba Shi, Ya ba Gwamna Hakuri

Bambarakwai: ‘Dan APC Ya Ki Amsar Mukamin da Aka Ba Shi, Ya ba Gwamna Hakuri

  • Gwamnatin Kebbi tayi wa Abubakar Bagudu Usman tayin kujerar Babban Mai taimakawa gwamna
  • Dallatun Kalgo yace bai bukatar wannan mukami, a mikawa matashi domin girma ya fara zuwan masa
  • ‘Dan siyasar ya rike kujera irin wannan tsakanin 2002 da 2006, yana ganin ya girmi wannan a yanzu

Kebbi - A ranar 27 ga watan Satumba 2022 aka ji cewa gwamnatin jihar Kebbi ta ba Abubakar Bagudu Usman mukamin mai bada shawara.

Kamar yadda muka samu labari daga shafin Salahuddeen Bala Bello a Facebook, Abubakar Bagudu Usman bai karbi wannan kujera ba.

Alhaji Abubakar Usman wanda yake rike da sarautar Dallatun Kalgon Bagudu ya nuna bai bukatar wannan matsayi da gwamna ya ba shi.

An nada Dallatun Kalgoa matsayin Babban Mai taimakawa gwamna Atiku Abubakar Bagudu, amma ya ga sam bai bukatar wannan mukami.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

A takardar da ya aikawa gwamnatin Kebbi, Abubakar Bagudu Usman yace ba zai karbi aikin ba saboda ya rike irin kujera a shekarun baya.

Zai zama ban-ba-ra-kwai, amma wannan ce matsayata. Watakila kuskure aka yi saboda:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Abubakar Bagudu Usman
Wasikar Abubakar Bagudu Usman Hoto: www.nairaland.com
Asali: UGC

Wasikar da Abubakar Bagudu Usman ya rubuta

1. Ban nemi mukamin ba.
2. Na rike wannan kujera shekaru 20 da suka wuce a 2002 a matsayin:
A. Babban mai taimakawa Gwamna a kan wayar da kan al’umma: 2002 – 2004
B. Babban mai taimakawa Gwamna a kan yada labarai: 2004
C. Babban mai taimakawa Gwamna a kan harkoki na musamman: 2005 - 2006
3. Ba na bukatar wannan aiki ido rufe, domin na rike mukamin a lokacin ina ganiyata.
4. Nayi matukar imani akwai matasa barkatai da za su rike wannan kujera da kyau fiye da mai shekara 55.
5. Ayyukan gabana sun ishe ni ba tare da na toshewa matasa masu tasowa masu jini a jiki damarsu ba.

Kara karanta wannan

Yadda Atiku Zai Bi Wajen Maganin Akidar Biyafara Da Tayi Shekara da Shekaru

6. Ni dai, nagode, amma dai nayi tsufa da wannan.
Nagode.
Abubakar Bagudu Usman
(Dallatun Kalgo)

Raini ko cin girma?

Da Legit.ng Hausa ta tuntubi Dallatun Kalgo, ya shaida mana cewa ba a tuntube shi ba, sai dai kurum ya ji an aiko masa da takardar ba shi mukami.

‘Dan siyasar yace yana tare da gwamnatin APC a Kebbi, amma ya bar kujerar ga masu jini a jikinsu. A shekara 55, yana ganin bai dace da ofishin ba.

Abubakar Bagudu yace da yana aikin watsa labarai, da ya zama babba a gidan jarida yanzu.

Ana neman su Hameed Ali

Kun samu labari ‘Yan Majalisar wakilan tarayya da na dattawa suna binciken kwangilar da gwamnatin tarayya ta ba Kamfanin Webb Fontaine.

Wannan ya sa ake bukatar ganin Shugaban kwastam, Kanal Hameed Ali, Gwamnan CBN da Ministar kudi su je gaban kwamitin hadaka na majalisa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel