Atiku, Kwankwaso, Da Sauran Yan Takara Sun Hallara Wajen Yarjejeniyar Zaman Lafiya, An Nemi Tinubu An Rasa

Atiku, Kwankwaso, Da Sauran Yan Takara Sun Hallara Wajen Yarjejeniyar Zaman Lafiya, An Nemi Tinubu An Rasa

  • Kamar yadda akayi a shekarar 2015 da 2019, yan takarar kujerar shugaban kasa sun hadu da juna a Abuja
  • Kwamitin Janar AbdusSalam Abubakar da Bishop Mathew Kukah sun shirya taron yarjrjrniyar zaman lafiya
  • Wannan ne na farko da za'a yi sannan a sake yin wani yayinda zaben ya gabato a 2023

Abuja - Wasu yan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2023 da shugabannin jam'iyyunsu 18 sun hallara a farfajiyar ICC dake birnin tarayya Abuja da safiyar Alhamis, 29 ga Satumba, 2022.

Jiga-jigan siyasan sun hadu ne domin rattafa hannu kan yarjejeniyar tabbatar da zaman lafiya yayinda aka fara yakin neman zaben 2023.

Kwamitin Zaman Lafiya ta kasa NPC karkashin jagorancin tsohon shugaban kasan mulkin soja, Janar AbdulSalami Abubakar ne ta shirya zaman.

Kara karanta wannan

2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

An kafa kwamitin NPC a 2014 bayan fargaban rikici a zaben 2015.

Yan takaran dake hallare a wajen sun hada Dan Takaran Shugaban Kasar AA, Manjo Hamza Al-Mustapha, Dan Takaran Jam'iyyar AAC, Omoyele Sowore, Dan Takaran Jam'iyyar NNPP, Rabiu Musa Kwankwaso, Dan Takaran Jam'iyyar LP, Peter Obi, da sauran su.

An nemi dan takarar jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu, an rasa amma an ga abokin tafiyarsa, Kashim Shettima.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

NPC CCt
Atiku, Kwankwaso, Da Sauran Yan Takara Sun Hallara Wajen Yarjejeniyar Zaman Lafiya, An Nemi Tinubu An Rasa Hoto: @MrBanksOmisore
Asali: Twitter

2023: Tinubu Ba Zai Samu Damar Sa Hannu Kan Wata Muhimmiyar Takarda ba

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ba samu damar saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta zaben 2023 ba.

Tinubu, wanda a yanzu haka yana kasar Birtaniya, ba samu halartar taron saka hannu kan yarjejeniyar da kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC) ya shirya ba,wanda shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ke shugabanta.

Tinubu ya bar Najeriya a ranar Lahadin da ta wuce inda ya gana da wasu kungiyoyi a kasar Birtaniya. Sai dai akwai hasashe cewa ya je neman magani ne kasar.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel