Atiku vs Wike: Gwamna Ortom Ya Raba Jiha Da Wike, Ya Ce Yana Tare Da Ayu

Atiku vs Wike: Gwamna Ortom Ya Raba Jiha Da Wike, Ya Ce Yana Tare Da Ayu

  • Gwamnan jihar Benue yace shi fa yana tare da shugaban jam'iyyar PDP, Iyorchia Ayu, ba Nyesom Wike ba
  • Wata kungiyar ta zargi Ortom da yaudarar Iyorchia Ayu wanda dan asalin jihar Benue ne
  • Dan takaran shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar, ya nada manyan jiga-jigan PDP matsayin mashawarta

Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, a ranar Litnin, ya yi watsi da rahotannin cewa yana goyon bayan tsige Shugaban uwar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Dr. Iyorchia Ayu.

Ortom yace ba zai yiwu ya goyi bayan cire Ayu ba saboda shi ya tabbatar da zamanshi shugaban jam'iyyar, rahoton ThisDay.

Ortom ya jaddada goyon bayansa ga Ayu, wannan ya nuna barrantarsa da gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike.

Ortom
Atiku vs Wike: Gwamna Ortom Ya Raba Jiha Da Wike, Ya Ce Yana Tare Da Ayu
Asali: UGC

Gwamnan ya bayyana hakan a martanin da yayi ga kungiyar Jemgbagh Development Association, dake zargin Ortom da hada kai da wasu wajen yiwa dan jiharsa zagon kasa.

Kara karanta wannan

Dailin Da Yasa Na Yi Shiru Game da Rikicin Atiku da Gwamna Wike, Saraki Ya Magantu

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Wannan sabon jawabi na Ortom ya nuna cewa ya daina goyon bayan Wike.

A jawabin da sakataren yada labaransa, Nathaniel Ikyur, ya fitar a ABuja, Ortom yace kowa ya sani cewa su sukayi aiki tukuru wajen tabbatar da cewa Ayu ya zama shugaban PDP.

"Saboda haka, ba zai yiwu gwamna ya juya masa baya yace sai an cireshi ba," cewar jawabin.

Ya karyata zargin kungiyar Jemgbagh na cewa da hannun Ortom cikin yunkurin tsige Ayu.

Atiku Ya Nada Saraki, Shekarau da Wasu Jiga-Jigan PDP a Wasu Muhimman Mukamai

Yayin da ake shirin fara kamfe na zaɓen 2023, mai neman zama shugaban ƙasa a inuwar PDP, Atiku Abubakar, ya yi sabbin naɗe-naɗe masu muhimmanci da nufin karfafa tawagar yaƙin neman zaɓensa.

Channels TV ta ruwaito cewa waɗanda Atiku ya naɗa sun haɗa da, tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, a matsayin wakilin ɗan takarar na musamman da Sanata Pius Anyim, a mukamin mashawarci na musamman.

Kara karanta wannan

Atiku Ya Yi Magana Bayan Fallasar Wike, Ya Bayyana Yadda PDP Za Ta Ci Zabe A 2023

Sauran waɗanda suka samu shiga a matsayin mashawarta na musamman sune, tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon gwamnan Osun, Prince Olagunsoye Oyinlola da kuma Sanata Ehigie Uzamere.

Asali: Legit.ng

Online view pixel