Jerin ’Yan Siyasar Najeriya 5 da Suka Mallaki Akalla Jiragen Sama 2 Masu Zaman Kansu

Jerin ’Yan Siyasar Najeriya 5 da Suka Mallaki Akalla Jiragen Sama 2 Masu Zaman Kansu

  • 'Yan siyasan Najeriya na daga cikin masu fantamawa a nahiyar Afrika saboda tsabar kudi da suka mallaka, ciki har da jirage masu zaman kansu
  • Tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff na daga cikin 'yan Najeriya da suka mallaki jirage nasu na kansu
  • Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Abia Orji Kalu na daga cikin wadanda suka mallaki jirage fiye da daya

Najeriya - Fantamawar rayuwa da mallakar jirgin hawa domin more rayuwa na daya daga cikin abubuwan da ake gani a matsayin tumbatsar dukiya a duniya, a Najeriya ma bata sauya zane ba.

A nan kasar, galibin wadanda suka mallaki kudin a zo a gani 'yan siyasa ne, don haka 'yan Najeriya ke musu kallon allunan duba idan ana maganar dukiya.

'Yan siyasan Najeriya da suka mallaki jirage da yawa
Jerin ’Yan Siyasar Najeriya 5 da Suka Mallaki Akalla Jiragen Sama 2 Masu Zaman Kansu | Hoto: @officialasiwajubat/@aatiku/@princenednwoko/oukgram
Asali: Instagram

Duk da cewa, ba lallai kace duk wani dan siyasa ya samu kudi daga shiga siyasa bane, amma dai a bayyane yake, a kasar nan 'yan siyasa sun fi rayuwar fantamawa.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Sun Gaji da Abubuwan da ke Faruwa a Kasar nan, Atiku

And one of the ways they flaunt their wealth is through ownership of expensive assets like private jets, luxury vehicles, and yachts.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A rahoton nan, mun tattaro muku jerin wasu 'yan siyasar da suka mallaki jirage na kansu.

1. Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya, Atiku Abubakar na daya daga cikin hamshakan attajirai a kasar

Ya yi mataimakin shugaban kasa ga a lokacin mulkin Olusegun Obasanjo tsakanin 1999-2007. Biloniya ne mai kasuwancin kayan ruwa, fannin ilimi da noma.

Yana da jirgi kirrar Embraer Phenom 100 da darajarsa ta kai da $4.5m. Haka nan ya mallaki jirgi kirar Bombardier Global 6000 da akalla kudinsa ya kai $21m; kiran 2012, kiran 2021 kuwa ya kai $64.30m a cewar wani rahoton Aircraft Bluebook a 2022.

2. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Tsohon gwamnan Legas, dan takarar shugaban kasa a APC kuma tsohon sanata, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ba boyayye bane a attajiran Najeriya.

Kara karanta wannan

Musulmi da Musulmi: Tsohon Sakataren Buhari Ya Fallasa Wasu Kulle-Kullen da Tinubu Ke Yi Gabanin 2023

Yana da jirgi kiran Bombardier Global Express XRS da kudinsa akalla ya kai $15m-$17m, nan ma kiran 2012. Hakazalika, yana da wani jirgin mai suna Gulfstream G650 da kudinsa ya kai $65m.

3. Ned Nwoko

Biloniya dan Najeriya, kuma tsohon sanata mijin 'yar wasan kwaiwayo Regina Daniels. na daga cikin masu jirage a Najeriya.

Yana da jirgi kiran Dassault Falcon 7x, wanda a cewar Aircraft Bluebook ya kai akalla $35m-$53m.

4. Ali Modu Sherif

Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sherif na daya daga cikin masu fada aji kuma hamshakan attajirai a Najeriya

Yana da jirage hudu. mallakinsa, daya daga ciki shi ne Gulfstream G650 da kuma wasu uku da ake kira Dornier.

5. Orji Uzor Kalu

Sanata Orji Ozor Kalu dai mutum ne da sunansa ya bazu a Najeriya, kuma tsohon gwamna ne da ya yi mulki har sau biyu a jihar Abia. Maganar kudi? Hamshaki ne shima.

Kara karanta wannan

Tikitin Musulmi Da Musulmi: Jerin Mukaman Da Kiristocin Najeriya Za Su Iya Samu A Gwamnatin Tinubu

Kalu ne ya kafa kamfanin nan SLOK Holdings kuma mamallakin shahararrun jaridun nan; Daily Sun da New Telegraph.

Jiragensa su ne Gulfstream G650 guda daya, Gulfstream IV guda uku da Bombardier Global Express XRS guda daya.

Matashi Ya Ba da Mamaki Yayin da Ya Sauya Motarsa Zuwa Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu

A wani labarin, Mithilesh Prasad, wani matashi mai shekaru 24 dan kasar Indiya ya baya da mamaki yayin da ya sauya motarsa zuwa jirgi mai saukar ungulu.

A wani rubutun Instagram da @trtworld ta yada, an ga yadda matashin ya yi ya cika burinsa na kera jirgi mai saukar ungulu.

Don tabbatar da motar tasa ta yi kamata da jirgi mai saukar ungulu, matashin ya yi sauye-sauye da dama, ciki har da lika bambam jirgi, farfela da dai sauransu. Sai dai, har yanzu jirgin bai fara tashi ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel