Matashi Ya Ba da Mamaki Yayin da Ya Sauya Motarsa Zuwa Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu

Matashi Ya Ba da Mamaki Yayin da Ya Sauya Motarsa Zuwa Jirgin Sama Mai Saukar Ungulu

  • Wani matashi ba'indiye mai suna Mithilesh Prasad ya sauya wata 'yar motarsa zuwa jirgin sama mai saukar ungulu
  • Matashin dan shekara 24 ya yiwa motar kare-karen jikin jirgin sama mai saukar ungulu, ya sauya baya da duk wasu bangarorin jikin motar
  • Duk da a yanzu ya yi nasarar kirkirar jirginsa na sama, ya bayyana cewa, yana da burin wata rana ya gina cikakken jirgi

Mithilesh Prasad, wani matashi mai shekaru 24 dan kasar Indiya ya baya da mamaki yayin da ya sauya motarsa zuwa jirgi mai saukar ungulu.

A wani rubutun Instagram da @trtworld ta yada, an ga yadda matashin ya yi ya cika burinsa na kera jirgi mai saukar ungulu.

Don tabbatar da motar tasa ta yi kamata da jirgi mai saukar ungulu, matashin ya yi sauye-sauye da dama, ciki har da lika bambam jirgi, farfela da dai sauransu. Sai dai, har yanzu jirgin bai fara tashi ba.

Kara karanta wannan

Dan Najeriya ya jawo cece-kuce yayin da ya fara birgima a kasa lokacin da matarsa ta haihu

Matashi ya sauya mota zuwa jirgi mai saukar ungulu
Matashi ya ba da mamaki yayin da ya sauya motarsa zuwa jirgin sama | Hoto: @trtworld
Asali: Instagram

Wannan jirgi dai na samar wa Mithilesh kudin shiga ta hanyar ba da hayansa a lokutan bukukuwa, musamman aure.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Matashin ya ce yana da burin wata rana ya kera jirgi sukutum.

Kalli bidiyon:

Martanin jama'a

@psean_the_artist yace:

"To ai zai iya yanke kan wani da wadannan farfelun."

@thekhanarbab yace:

"Jira nike tun tuni naga jirgin ya fire, gazawarku ta kada ni TRT."

@madebyeaq yce:

"Hanya mafi sauku wajen sheke mutanen da kake fushi dasu a kan titi."

@hatebuster3300 yace:

"Na sha mamakin ba'indiye mai tallan abinci a bakin hanya yanzu kuma na gaza magana da ganin jirgi mara tashi da aka yi don biki."

@f.ar.han_.sa.mi_ yace:

"Ya yi kusan irin abin da nake fatan yi. Aiki ya yi kyau dan uwa."

@im.umar.qadri yace:

"Na tuna wani dan Indiyan da ya kera jirgi mai saukar ungulu, amma ya mutu garin gwada tashi Na tausaya masa."

Kara karanta wannan

Harin 9/11 Na Amurka: Fasto Adebayo Ya Bayyana Yadda Aka Bincike Shi Saboda Yunkurin Siyan Jirgi

Yaro Dan Tsugugi Ya Jawo Magana, Ya Sa Mahaifiyarsa Kunci Yayin da Ya Zubar da Manjan N4K

A wani labarin, an ga wani yaron da ya damalmale jikinsa da manja a wani bidiyon da jama'ar intanet suka shiga mamakin gani.

A bidiyon da Mmasi Ivan ya yada a TikTok, an ga yaron yayin da yake wasa da manja a kasan daben cikin gida.

Kamar dai wanda ya samu ruwa da soso da sabulu, yaron ya zauna dabas tana wanke jikinsa da manjan tas.

Asali: Legit.ng

Online view pixel