Shugaba Buhari Ya Tafi Amurka Halartan Taron UN, Zai Dawo Bayan Mako Guda

Shugaba Buhari Ya Tafi Amurka Halartan Taron UN, Zai Dawo Bayan Mako Guda

  • Shugaban kasa Najeriya, Muhammadu Buhari, ya tafi Amurka halartan taron ganganmin majalisar dinkin duniya
  • Shugaban kasan ya samu rakiyar uwargidarsa, Aisha Buhari, wasu gwamnoni, ministoci da manyan jami'an gwamnati
  • Shugaban Bihari zai yi mako guda daya a Amurka kuma ya dawo kasar ranar Litnin, 26 ga Satumba

Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi birnin New York kasar Amurka Yau Lahadi, 18 ga watan Satumba, don halartan taron gangamin majalisar dinkin duniya (UNGA77).

A bisa bidiyon tashin jirgi shugaban kasa a tashar jirgin kasa da kasa ta Nnamdi Azikwe dake Abuja da Aminiya ta fitar, Ministan Abuja da manyan jami'an Sojoji sun yi masa Allah ya kiyaye hanya.

Buhari goes
Shugaba Buhari Ya Tafi Amurka Halartan Taron UN, Zai Dawo Bayan Mako Guda Hoto: Presidency
Asali: Facebook

Abinda Buhari Zai Yi A New York

Jiya, mai magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana cewa abubuwan da za'a tattauna a taron gangamin sun hada da rikicin Rasha da Ukraine, sauyin yanayi, annobar Korona, da makamashi.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaba Buhari Zai Tafi Amurka Halartan Taron UN Gobe Lahadi

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaba Buhari zai gabatar da nasa jawabin ranar Laraba, 21 ga Satumba, 2022.

Bayan jawabin, Adesina yace Buhari zai halarci wasu taruka da ganawar diflomasiyya da shugabannin duniya, yan kasuwar, da kungiyoyi.

Shugaban kasan zai samu rakiyar uwargidarsa, Aisha Buhari, wasu gwamnoni, ministoci da manyan jami'an gwamnati.

Ya ce Shugaban kasa zai dawo kasar ranar Litnin, 26 ga Satumba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel