Jerin Shugabannin Kasan Da Aka Gayyata Jana'izar Sarauniya Elizabeth, Akwai Buhari

Jerin Shugabannin Kasan Da Aka Gayyata Jana'izar Sarauniya Elizabeth, Akwai Buhari

Daga karshe, za'a yi jana'izar Sarauniyar Elizabeth II ranar Litinin 19 ga watan Satumba, 2022 a kasar Ingila.

Kamfanin yada labaran kasar Birtaniya, BBC, ya ruwaito cewa a karshen makon da ya gabata aka aika takardun gayyatar zuwa jana'izar ga shugabanni da sarakuna da sauran manyan mutane a fadin duniya,

Rahoton ya kara da cewa akalla shugabannin kasashe da manyan mutane fiye da 500 ake kyautata zaton za su halarci jana'izar.

Daga cikin sharrudan da gwamnatin Birtaniya tayi shine babu shugaban kasar da zai halarci jana'izar da jirginsa, kowa jirgin kasuwa zai shiga.

Daga nan sai Motar Bas ta kwashi shugabannin kasan zuwa yammacin Landan.

Za a yi taron a babban dakin Westminster Abbey daukar mutum 2,200.

Daga cikin wadanda aka gayyata akwai sarakuna da shugabannin kasa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Wani Abu Ya Fashe da Mutane, Ya Yi Mummunar Ɓarna a Jihar Jigawa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Queen
Jerin Shugabannin Kasan Da Aka Gayyata Jana'izar Sarauniya Elizabeth, Akwai Buhari
Asali: UGC

Ga jerin sunayen Sarakuna da aka gayyata:

  1. Sarkin Belgium Philippe da Sarauniya Mathilde
  2. Sarkin Netherlands Willem-Alexander da matarsa, Sarauniya Maxima
  3. Sarki Felipe da Sarauniya Letizia na Sifaniya
  4. Iyalan gidan sarautar Norway, Sweden, da Denmark

Ga jerin sunayen Shugabanin kasashen da aka gayyata:

  1. Shugaba Joe Biden tare da mai dakinsa Jill Biden
  2. Firaiministan Australia Anthony Albanese
  3. Firaiministar New Zealand Jacinda Ardern
  4. Firaiministar New Zealand Jacinda Ardern
  5. Firaiministar Canada Justin Trudeau
  6. Firaministar Bangladash Sheikh Hasina
  7. Shugaban kasar Sri Lanka Ranil Wickremesinghe
  8. Firaiministan India Narendra Modi
  9. Firaiministan Ireland Micheal Martin,
  10. Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier
  11. Shugaban kasar Italiya Sergio Mattarella
  12. Shugabar majalisar tarayyar Turai Ursula von der Leyen
  13. Shugaban kasar Koriya ta Kudu Yoon Suk-Yeol
  14. Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro
  15. shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan
  16. Shugaban Faransa Emmanuel Macron
  17. Shugabannin kasashen Commonwealth

Asali: Legit.ng

Online view pixel