Yar Yarinya Ta Fashe Da Kuka Yayinda Aka Kaita Gidan Marayu, Ta Bada Tausayi
- Wata kyakkyawar marainiya ta baiwa mutane tausayi yayinda wasu suka kaita gidan marayu
- A bidiyon da ya bazu a kafafen ra'ayi da sada zumunta, yar yarinyar ta fashe da kuka yayinda ake lallashinta
- Jama'a sun bayyana ra'ayoyinsu game da wannan bidiyo yayinda wasu ke cewa a kawo musu ita zasu dauki nauyinta
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Wata yarinya ta fashe da kuka lokacin da aka kaita gidan marayu inda zata koma zama.
A bidiyon da ya ya'du, yarinyar ta bada tausayi yayinda wadanda ke wajen suke kokarin bata hakuri suna share mata hawaye.
Gidan marayun Godsgrace_Orphanage ya daura bidiyon a Instagram yana mai neman taimako da sadaka daga wajen jama'a.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Masu gidan marayun sun kara da cewa yarinyar ta fara sabawa da wajen kuma ta rage kuka yanzu.
Kalli bidiyon:
Mutane sun tofa albarkatun bakinsu
Hauwa Yunusa:
Rashin iyaye masifane, Allah ya qarawa namu tsawon Rai Wanda suka rasa nasu ya Allah ka gafarta musu very heart touching
Sulaiman Isah Abubakar:
Subhanallah! Har naji tausayinta wllh, Allah ubangiji ka jigan iyayenmu baki daya
Muhd Wais Muhd:
Allah sarki rayuwa kenan, Allah ya rayaki ya kuma shirya akan sunnahr manzo S.A.W
Aisha Usman Adam:
Allahu akbar. Allah ka qarawa iyayenmu lpy da nisan kwana alfaran Annabi SAW
Fatima Marainiya:
Dan Allah wane gidan marayu ne a wane gari yake ku taimakamin da full address
Muhammad Nasir:
Ikon allah kaman wannan yarinyar a rasa wadda zai dauki nauyin ta a gidansa wai har sai an kaita gidan marayu. Wa iyazubillah wlh jama'a in har bamu gyara mun tallafawa marayu ba wlh mucire ran ganin daidai a rayuwa.
Alhassan Saleh Isah:
"ALLAH sarki tayi hakuri Muma mundandani maraicinnan yanzu komai yazama tarishi Allah SA mucika da imani"
Asali: Legit.ng