Allah Ya Yiwa Sarkin Funukaye, Alhaji Muhammad Muazu Kwaranga, rasuwa

Allah Ya Yiwa Sarkin Funukaye, Alhaji Muhammad Muazu Kwaranga, rasuwa

Innalillahi wa'inna'ilaihi raji'un

Allah ya yiwa Maimartaba Sarkin Funakaye Alhaji Muazu Mohammed Kwairanga rasuwa a daren Lahadi, 28 ga watan Agusta, 2023.

Hadimin Gwamnan jihar Gombe, Abdul No Shaking, ya bayyana hakan a jawa da ya fitar na ta’ziyya.

Yace za ayi jana’iza karfe 2pm a kofar fadan Sarkin.

A cewarsa,

INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJI'UN
Allah ya gafartawa Mai Martaba Sarkin Funakaye Alhaji Mu'azu Mohammed Kwairanga,

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Za'ayi Jana'izarsa Yau lahadi da Misalin karfe 2:00 na Rana a kofar fadar Sarkin dake garin Bajoga.
Allah Ya Jikanka da Rahama, Allah Yasa Aljannah Firdaussi ce Makomarsa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel