An Bindige Jami'an Yan Sanda 2 Har Lahira A Jihar Plateau

An Bindige Jami'an Yan Sanda 2 Har Lahira A Jihar Plateau

  • Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun halaka jami'an yan sandan Najeriya biyu a Jihar Plateau
  • An rahoto cewa sun bude wa yan sandan biyu wuta ne a yayin da suke bakin aiki a Kuru, suka kuma dauke bindigunsu
  • Abubakar Abdulkarim, kawun daya daga cikin jami'an yan sandan da aka kashe ya ce tuni an yi wa marigayin jana'iza

Jihar Plateau - An bindige wasu jami'an yan sandan Najeriya su biyu a bakin aikinsu a garin Kuru da ke karamar hukumar Riyom na jihar Plateau.

Taswirar Plateau
An Bindige Jami'an Yan Sanda 2 Har Lahira A Jihar Plateau. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

Wakilin Daily Trust ya gano cewa yan bindigan sun yi awon gaba da bindigun yan sandan da suka kashe.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Karfin hali: Dalibin kwaleji ya yI barazanar sace 'Provost', ya shiga hannun hukuma

Kawun daya cikin yan sandan da aka kashe ya magantu

Abubakar Abdulkarim, kawun daya daga cikin yan sandan da suka rasu ya shaidawa Daily Trust cewa lamarin ya faru na a wani shingen bincike da ke kusa makarantar sakandare ta kimiyya na gwamnati.

Ya kara da cewa an harbi dan uwansa Mukhtar Hassan sau biyu kuma akwai harsashi a jikinsa.

Abdulkarim ya ce an birne Hassan bisa koyarwar addinin musulunci, ya kara da cewa kafin rasuwarsa, dan uwan nasa na aiki ne da sashin yaki da yan ta'adda na rundunar yan sandan a jihar.

Yan Bindiga Sun Kai Wa Yan Sanda Hari, Ana Fargabar Wasu Sun Mutu

A wani rahoton, yan bindiga sun kai hari shingen binciken yan sanda suka kashe biyu cikinsu da wasu a garin Enugu, babban birnin Jihar Enugu.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis da safe a Gariki, MTD a karamar hukumar Enugu South a babban birnin jihar kamar yadda The Punch ta rahoto.

Kara karanta wannan

An Kuma: 'Yan Bindiga Sun Sake Yin Garkuwa da Matafiya da Dama a Jihar Arewa

A lokacin hada wannan rahoton, majiyoyi sun shaida wa wakilan Punch cewa ana nan ana harbe-harbe a iska a yayin da mutane ke tserewa don neman mafaka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel