Zukekiyar Diyar Gwamna Atiku Bagudu Za Ta Shiga Daga Ciki, Kyawawan Hotunanta Da Angonta Sun Bayyana

Zukekiyar Diyar Gwamna Atiku Bagudu Za Ta Shiga Daga Ciki, Kyawawan Hotunanta Da Angonta Sun Bayyana

  • Gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu zai aurar da kyakkyawar diyarsa, Maryam Bagudu
  • Za a daura Auren Maryam da angonta Ibrahim a karshen makon nan, kuma tuni aka fara shagali
  • A cikin hadaddun hotunan 'Dina' da ya yadu, an gano amaryar da angonta ciki shiga na bakakken kaya inda suka fito shar da su

Kebbi - Maryam Atiku Bagudu, kyakkywawar diyar gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu, za ta shiga daga ciki.

Za a daura auren Maryam da kyakkyawan angonta Ibrahim a cikin wannan makon, kuma tuni shagalin biki ya kankama.

Maryam Bagudu da Ibrahim
Zukekiyar Diyar Gwamna Atiku Bagudu Za Ta Shiga Daga Ciki, Kyawawan Hotunanta Da Angonta Sun Bayyana Hoto: northern_hypelady
Asali: Instagram

An gudanar da liyafar ‘Dina’ inda ango da amarya suka fito shar dasu cikin shiga da alfarma.

A cikin hotunan da shafin northern_hypelady ya wallafa a Instagram, an gano su cikin shiga ta bakakken kaya su dukka, yayin da amaryar ta sanya doguwar riga , ango Ibrahim ya yi shigar turawa ta kwat da wando.

Kara karanta wannan

Shawari kyauta: Hanyoyi 15 da za ku bi domin kiyaye kanku daga fadawa matsala a Najeriya

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ga hotunan a kasa:

Tunda Kunzo A Daura Kawai: Daga Zuwa Kai Gaisuwa, Iyaye Sun Nemi A Shafa Fatiha Kowa Ya Huta, Bidiyo

A wani labarin kuma, mun ji cewa mabiya shafin Twitter sun tofa albarkacin bakunansu bayan samun labarin wani aure da aka kulla ba tare da shiri ba kuma cikin sauki a karshen makon jiya.

Kamar yadda wani matashi mai suna Mista Bukhari Suwaid da shafin @suwaidybaba a Twitter ya bayyana, ya ce sun raka wani abokinsa gidan iyayen budurwar da yake nema da nufin gaisuwa.

Sai dai da isarsu gidan, sai iyayen suka nemi su je su zo da goro inda suka shiga kaduwa matuka. Bayan nan sai suka yi kamar yadda aka umurce su inda suka siya goro suka kai tare da bayar da kudin sadaki gaba daya.

Kara karanta wannan

An Kafa Kwamitin Mutum 14 da Zai Kawo Karshen Rikicin Atiku da Wike a PDP

Asali: Legit.ng

Online view pixel