Yan Bindiga da Masu Kai Musu Bayanai Za Su Fuskanci Hukuncin Kisa, Inji Matawalle Na Zamfara

Yan Bindiga da Masu Kai Musu Bayanai Za Su Fuskanci Hukuncin Kisa, Inji Matawalle Na Zamfara

  • Gwamnan jihar Zamfara ya ce ya samu mafita ga matsalar tsaro da ta addabi jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya
  • A daya daga cikin matakan, ya ce za a fara yankewa duk wanda aka kama da laifin bindiganci hukuncin kisa
  • Ana yawan samun hare-haren 'yan bindiga a yankunan Katsina, Zamfara, Niger da dai sauran jihohin makwabta

Jihar Zamfara - Gwamnatin jihar Zamfara ta rattaba hannu a kan hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da laifin aikata fashi da makami, satar shanu, tsafi, ko kai wa 'yan bindiga bayanan sirri.

Gwamna Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a wani sako da ya sanarwa al’ummar jihar a safiyar ranar Talata 16 ga watan Agusta, Punch ta ruwaito.

Gwamna Matawalle ya gani mafita ga matsalar tsaro da 'yan bindiga
'Yan bindiga da masu kai musu bayanai za su fuskanci hukuncin kisa, inji Matawalle na Zamfara | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Matawalle ya ce:

“A ranar 28 ga watan Yuni na wannan shekara, na sanya hannu kan kudirin dokar haramtawa da hukunta masu fashi da makami, satar shanu, tsafi, garkuwa da mutane da sauran laifukan da sukashafe su, 2022.

Kara karanta wannan

Duk wanda aka gani a harbe: Gwamnatin Zamfara ta haramta hawa babura a wasu yankuna

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Dokar ta ba da wata ka’ida ta doka na hukunta masu aikata laifin fashi da makami.
“Bisa ga sabuwar dokar, duk wanda aka samu da laifin aikata fashi, garkuwa da mutane, satar shanu, tsafi, ko kuma yin aiki a matsayin mai ba da bayanai ga ‘yan bindiga zai fuskanci hukuncin kisa.
"Hakazalika, duk wanda aka samu da laifin tallafawa ta kowacce fuska ga laifukan da aka ambata zai fuskanci hukuncin daurin rai da rai, ko dauri a gidan yari na shekaru 20, ko kuma a dauri a gidan yari na shekaru 10, ba tare da zabin tara ba."

Dalilin daukar wannan mataki

Gwamnan ya bayyana cewa matakan na daga cikin kokarin gwamnatinsa na ganin an shawo kan matsalar ‘yan bindiga da suka addabi jihar da kuma jihohin Arewa maso Yammacin kasar nan sama da shekaru goma.

Kara karanta wannan

Karshen alewa: Kotu ta yankewa kasurgumin dan bindiga hukuncin zaman gidan magarkama

Ya ci gaba da cewa tun daga lokacin da gwamnatinsa ta kafu ya fara bullo da dabarun dakile matsalar ‘yan bindiga a fadin jihar.

Ya kara da cewa:

"Abin farin ciki, sabbin matakan sun fara samar da sakamakon da ake so duk kuwa da hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa nan da can."

Gwamnan ya bayyana ayyukan masu kai bayanai ga 'yan bindiga a matsayin wani babban sauyi na magance kalubalen rashin tsaro a jihar, inda ya bayyana kwarin gwiwar cewa nan ba da jimawa ba lamarin zai zama tarihi.

Ya kara da cewa:

“Game da batun masu kai bayanai, wanda shi ne babban abin da ke kawo cikas wajen yaki da ‘yan bindiga, ina mai farin cikin sanar da jama’ar jihar Zamfara masu son zaman lafiya cewa mun yi nasarar cafke da yawa daga cikinsu.
"A halin yanzu ana yi musu tambayoyi kafin a gurfanar da su a gaban kuliya kamar yadda doka ta tanada."

Kara karanta wannan

Abuja: An kame wasu mutane 480 da ake zargin sun tsere daga magarkamar Kuje

A baya dai Matawalle ya bayyana goyon bayansa a baya kan hukunta masu aikata bindiganci, Daily Post ta ruwaito.

An Yankewa Kasurgumin Mai Garkuwa da Mutane Wadume Hukuncin Shekaru 7 a Magarkama

A wani labarin, babbar kotun Abuja karkashin mai shari'a Binta Kyako ta yankewa kasugumin dan bindigan da ya addabi wani yankunan jihar Taraba.

Bayan shafe lokaci ana shari'a, an kama Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume da laifukan da ake tuhumarsa, kana aka daure shi zaman shekaru bakwai a gidan yari.

Rahoton da muke samu ya bayyana cewa, Wadume zai yi zaman magarkama ne tare da wasu mutane biyu da ake tuhumarsu tare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.