Yan Ta'adda Sun Rika Mana Wa'azi Lokacin Muna Hannun Su, Fasinjan Jirgin Ƙasa

Yan Ta'adda Sun Rika Mana Wa'azi Lokacin Muna Hannun Su, Fasinjan Jirgin Ƙasa

  • Masu garkuwa damu sun rinka mana wa'azin da ƙara mana kwarin guiwar yin addu'a a sansanin su, inji Fasinjan da ya kuɓuta
  • Hassan Aliyu, ya ce su kan jawo ayoyin Alƙur'ani yayin da suke magana, ya labarta wani musu da suka taɓa yi
  • A watan Maris, Yan ta'adda da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka farmaki Jirgin ƙasan Kaduna-Abuja

Kaduna - Hassan Aliyu, ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin kasan Kaduna-Abuja wanda ya shafe kwanaki a hannun yan ta'adda da abokin aikinsa ɗan Fakistan, ya ce lokacin suna tsare, masu garkuwa sun rika musu wa'azi.

A cewar Fasinjan, wanda suka kubuta bayan doguwar tattauna wa da maharan, ya ce suna musu wa'azi kuma suna tunatar da su game da yin Sallah da Addu'a.

Harin jirgin ƙasan Kaduna.
Yan Ta'adda Sun Rika Mana Wa'azi Lokacin Muna Hannun Su, Fasinjan Jirgin Ƙasa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

A wata hira da Daily Trust, Aliyu ya ce ba su taba samun matsala kan batun yin Sallah ba saboda lokuta da dama masu garkuwa da su ke ƙara musu kwarin guiwar su yi Addu'ar neman kubuta.

Kara karanta wannan

Abun tausayi: Fasinjan Jirgin Ƙasan Kaduna Ya faɗi Manyan Ayyuka Biyu da Yan Ta'adda Suka Sanya Su

A kalamansa ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Bamu samu matsala da Sallah ba, ba wanda ya taɓa mu game da ita, kawai bamu da yanci, duk abinda zaka yi dole ka nemi izini, duk inda zaka je sai ka nemi izini, lokaci ɗaya da ba sai mun nemi izini ba shi ne idan zamu tattauna tsakanin mu."

Yadda Suke Mana Wa'azi

Aliyu ya ƙara da cewa yan ta'addan da suka yi garkuwa da su, sun rika yi musu wa'azi, suna jawo ayoyin Alƙur'ani.

"Ina tuna wani lokaci da wani ya ce akwai wata aya a Alƙur'ani da tace 'Ya kamata ku kira mutane zuwa Addinin Allah da hikima kuma ku tambaye su meyasa suke aikata aikin da suke yi."
"Mai Wa'azin ya maida amsa da cewa ba bu wani wuri da ayoyi biyu suka ci karo da juna a Alƙur'ani cewa kafin a kira kowane mutum kafiri, wajibi a koya wa wannan mutumin Musuluncin da farko.

Kara karanta wannan

Mutumin da aka daba wa wuka saboda batanci ga Annabi na can asibiti rai hannun rabbaba

"Muka ƙi yarda, abun gunin sha'awa, zasu zo da daddare ko da rana mu tattauna, sukan tambaye mu ko mu mu tambaye su kuma zasu ba da masa cikin fara'a."

A wani labarin kuma 'Yan Bindiga sun kai sabon hari makarantar sakandire a jihar Arewa, sun aikata mummunar ɓarna

Yan bindiga sun kai sabon hari GSS Nassarawa-Eggon, a jihar Nasarawa, sun harbe wani malami ɗaya har lahira.

Wani malami da ya memi a ɓoye bayanansa ya ce maharan sun kutsa makarantar da daren Asabar kuma suka nufi gidan mamacin kai tsaye.

Asali: Legit.ng

Online view pixel