Muna Debo Ruwa da Yo Itace Yayin da Mata Ke Dafa Abinci, Fasinjan Jirgin Kasa

Muna Debo Ruwa da Yo Itace Yayin da Mata Ke Dafa Abinci, Fasinjan Jirgin Kasa

  • Bayan ya samu yanci, ɗaya daga cikin fasinjojin jirgin ƙasan Kaduna ya bayyana ayyukan da suka yi a hannun yan ta'adda
  • Hassan Aliyu, ya ce tsawon kwanaki 70 da ya shafe a mafakar su, kullum maza ke ɗebo ruwa mata kuma su dafa abinci
  • A watan Maris da ya gabata, wasu yan ta'adda suka farmaki jirgin ƙasan Kaduna zuwa Abuja, suka sace Fasinjoji

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Ɗaya daga cikin Fasinjojin jirgin Kaduna zuwa Abuja da yan ta'adda suka sace a watan Maris, Hassan Aliyu, ya ba da labarin irin bautar da suka sha lokacin da suke tsare.

A wata hirar bayan fage da jaridar Daily Trust, Aliyu ya ce tsawon kwanaki 70 da ya shafe a mafakar yan ta'adda, shi da sauran mutane na cin wata matalauciyar Shinkafa da Tuwo, abincin gargajiya.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Yi Garkuwa da Yan Kwallon Najeriya Mata, Sun Nemi Kuɗin Fansa

Harin jirgin ƙasan Kaduna.
Muna Debo Ruwa da Yo Itace Yayin da Mata Ke Dafa Abinci, Fasinjan Jirgin Kasa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya ce yayin da matan cikin su ke aikin girki kullum, kana su yi wanke-wanke, su kuma maza suke zuwa su nemo itace sannan kuma su ɗebo ruwa a kowace rana.

Aliyu ya ce:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Muna cin abinci kaɗai domin mu rayu, suna bamu isasshen abinci, suna ciyar damu yadda ya kamata idan ana maganar yawa. Muna da shinkafa da aka dafa da Mai da Maggi, ɗayan zaɓin kuma shi ne Tuwon Masara."

Yadda Muka rayu ba yanci - Aliyu

Aliyu ya ƙara da cewa ba su samu matsala game da Ibadar Allah ba, kuma yan ta'addan ba su ci mutuncin su ta kowane fanni ba, inda ya kara da cewa kawai ba su da yanci, ko me zaka yi sai ka nemi izini.

A zantawarsa da jaridar, Aliyu ya cigaba da cewa:

Kara karanta wannan

Bidiyo: An Kai Hari Ga Salman Rushdie, Shahararren Marubucin Da Ya Yi Batanci Ga Annabi SAW

"Duk abinda zaka yi tilas ka nemi izini, abu ɗaya da ba sai mun nemi izini ba shi ne idan zamu tattauna tsakaninmu. Ba maganar canza tufafi saboda ba mu zo da ko ɗaya ba."
"Zamu je rafi, mu yi wanka mu wanke kayan mu, mu jira su bushe, sannan mu dawo, sun tanazar mana Sabulu."

Yadda muka rayu da aka fara ruwan sama

Lokacin da aka fara ruwan sama, Aliyu ya ce akwai wasu runfar kwano da suka yi, uku ko huɗu, "Duk can muka koma, mata suka ɗauki ɗaya, daga baya suka zo suka gina mana babba, idan ruwa be ɗauke ba can muke kwana."

"Wajajen karfe Shida ko ta wuce haka, na ɗauka ba zamu tafi ba sai washe gari saboda ana ruwa. Ba zato muka samu umarnin mu fito, da muka fito aka ɗauke mu a Babur, sai da muka yi tafiyar awanni Shida da dare, muna tsallaka rafuka."

Kara karanta wannan

Wasu Mutum Uku Sun Tsallake Rijiya da Baya a Hannun Mutane Bayan Asirin Su Ya Tonu a Abuja

A wani labarin kuma Sojojin sama da ƙasa sun hallaka dandazon yan ta'adda a Kaduna, Sun kwato makamai

Sojojin Sama da Ƙasa sun yi luguden wuta kan sansanin yan ta'adda a yankin karamar hukumar Chikun jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaro, Samuel Aruwan, ya ce sojojin sun hallaka yan ta'adda da dama, sun kwato makamai da sauran su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel