Jerin Kayayyaki 8 da Hukumar Kwastam Ta Najeriya Ta Haramta Fitar da Su Waje

Jerin Kayayyaki 8 da Hukumar Kwastam Ta Najeriya Ta Haramta Fitar da Su Waje

  • Tun farkon hawan shugaban kasa Muhammadu Buhari aka fara kawo sabbin dokoki masu tsauri game da shige da ficen kayayyaki a Najeriya
  • Hukumar Kwastam ta bayyana wasu kayayyaki da ta haramta fita dasu daga Najeriya saboda wasu dalilai na fasa kwabri
  • A baya hukumar ta NCS ta bayyana kame wasu tirelolin shinkafa da aka shigo dasu daga kasar waje

FCT, Abuja - Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta bayyana jerin kayayyaki da aka haramta fitar da su daga Najeriya zuwa wasu kasashen na ketare.

Duk wani yunkuri na fitar da kayayyakin da ta jero ko safarar su ta kan iyaka ba bisa ka'ida za a dauki doka akai kuma za a hukunta duk da ya kuskura ya gwada bisa tanadin dokar Najeriya da aka shar'anta.

Kwastam ta bayyana kayayyakin da ta haramta fita dasu daga Najeriya
Jerin Abubuwa Guda 8 da Hukumar Kwastam Ta Najeriya Ta Haramta Fitar da Su | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Ga jerin kayayyakin kamar haka:

Kara karanta wannan

Rudani: Hukumar SSS ta janye kara kan mai tattaunawa da 'yan bindiga, Tukur Mamu

  1. Masara
  2. Katako (guma-gumai ko wanda aka sarrafa)
  3. Fatun da ba a sarrafa ba tare da ba su lambobin H.S. 4101.2000.00 - 4108.9200.00
  4. Kayan tarkacen karafa
  5. Kayyaki da nau'ikan roba da ake cire daga albarkatun kasa wadanda ba a sarrafa ba
  6. Kayayyakin tarihi da ababen tunawa
  7. Namun dajin da aka ambata a matsayin nau'in da ka iya bata nan kus, misali; Kada, Giwa, Kadangare, Mikiya, Biri, Jakin daji, Zaki da sauransu.
  8. Duk kayan da aka shigo dasu cikin Najeriya daga wasu kasashen

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tuni dama NCS ta fara gwanjon haramtattun kayayyaki ta yanar gizo da suka hada da manyan motoci iri daban-daban, da aka kama daga hannun masu fasa kwauri a Imo/Abia da kuma Edo/Delta.

Wakilinmu ya tattauna da wani mai sana'ar jari-bola a jihar Gombe, Adamu Muhammad Sani, wanda ya bayyan kadan daga sirrin kasar karafa.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Kotun daukaka kara ta tabbatar da hukuncin dauri kan dan tsohon shugaban fansho

Ya ce:

"Duk da haka fitar kaya da aka yi, kayan na kara tsada, saboda a da Kano muke kai wa, yanzu har nan shagona dan China ke zuwa yana saye.
"Zan iya ce maka kasuwar tana nan yadda take a baya, sai dai ma karin albarka da muke gani."

Kwastam ta kama tireloli 12 makare da buhunan shinkafar waje mai guba

A wani labarin, hukumar Kwastam ta Zone A ta sanar da kama buhunan shinkafa 7,259 na kasar waje mai nauyin kilogiram 50, kwatankwacin manyan motoci tireka 12 a watan Afrilun 2022.

Hukumar ta ce, rundunar ta kama wasu mutane 12 da ake zargi da shigo da haramtattacciyar shinkafar da sauran kayayyaki.

Da yake zantawa da manema labarai a sashin a ranar Alhamis, 5 ga Afrilu, 2022, Kwanturolan Hukumar Kwastam mai kula da sashin, Hussein Ejebunu ya bayyana cewa an gano buhunan shinkafar da ba su dace da cin dan Adam ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya tona sirrin gwamnoni, ya ce ba zai yi Allah wadai da wata kasurgumar kungiyar ta'addanci ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel