SSS Ta Janye Kara Kan Mai Tattaunawa Da ’Yan Bindiga, Tuku Mamu

SSS Ta Janye Kara Kan Mai Tattaunawa Da ’Yan Bindiga, Tuku Mamu

  • Hukumar DSS ta bayyana janye karar da ta shigar kan mai kamfanin jaridar Desert Herald, Alhaji Tukur Mamu
  • An tsare Mamu ne saboda zargin yana hannu a ayyukan ta'addanci da ke faruwa a Arewacin Najeriya a shekarun nan
  • Mamu ne wanda ke tattaunawa da 'yan bindigan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna a tsakiyar shekarar nan

Hukumar tsaro ta farin kaya (SSS) a ranar Alhamis ta bayyana janye bukatar ci gaba da tsare Tukur Mamu, tsohon mai shiga tsakanin 'yan bindiga na sama kwanaki 60 bayan kama shi.

Idan baku manta ba, an kama Mamu ne a watan Satumba a kasar Masar bisa zargin hannu a ayyukan ta'addanci, Premium Times ta ruwaito.

Mamu na daya daga cikin wadanda ke tattaunawa da 'yan bindigan da suka sace fasinjojin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: EFCC ta sake gurfanar da wani fitaccen tsohon gwamnan Arewa a gaban kotu

Bayan kamo Mamu daga Masar, an dawo dashi Najeriya domin gaba da bincike tare da gano alakarsa da wasu tsageru.

An janye kara kan Alhaji Tukur Mamu
SSS Ta Janye Kara Kan Mai Tattaunawa Da ’Yan Bindiga, Tuku Mamu | Hoto: neptuneprime.com.ng
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

An gano makamai da kudade a gidan Tukur Mamu

SSS ta ce gano wasu makamai da tarin kudi a gidan Mamu, lamarin da yasa hukumar ta nemi kotu ta ba ta damar ci gaba da tsare shi na tsawon kwanaki 60 ko sama saboda bincike.

Kotun ta saka ranar Alhamis domin ci gaba da sauraran bukatar hukumar kan abin da ta nema a tun farko, Neptune Prime ta tattaro.

Sai dai, a sake zaman da aka yi , lauyan SSS, A.M Danlami ya shaidawa mai shari;a Nkeonye Maha cewa, jim kadan bayan gabatar da bukatar, SSS ta nemi a janye karar.

Mr Danlami ya ce, akwai abubuwan da suka faru da yasa hukumar ya janye lamarin.

Kara karanta wannan

Yan Bindiga Sun Sace Dan Takarar Majalisa A Hanyarsa Na Zuwa Ganin Wakilan Akwatin Zabe

Daga nan ne mai shari'a ya amince da janye batun a gaban kotu.

Bana tsoron komai, cewar Tukur Mamu bayan da aka kwamushe shi

A tun farko, Tukur Mamu ya ce bai jin tsoron komai da zai iya biyowa baya matukar lamari ne na bincike da ake yi a kansa.

Ya bayyana hakan ne jim kadan bayan kamo shi tare da dawo dashi Najeriya daga kasar Masar a watan Satumba.

An kama Mamu ne a hanyarsa ta zuwa Saudiyya, wanda hukumar SSS tace tana zargin zai tafi ganawa da wasu shugabannin 'yan ta'adda ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel