Kwastam ta kama tireloli 12 makare da buhunan shinkafar waje mai guba

Kwastam ta kama tireloli 12 makare da buhunan shinkafar waje mai guba

  • Hukumar Kwastam ta Najeriya reshen Zone A, ta ce ta kama kimanin tirela 12 na shinkafa mai guba
  • Hukumar ta ce an kama mutane kusan 12 da shigo da shinkafar da sauran haramtattun kayayyaki
  • Shugaban Hukumar Kwastam na yankin, ya ce binciken da aka yi a dakin gwaje-gwaje ya tabbatar da cewa shinkafar da aka kama tana dauke da gubar da bai kamata a ci ba

Legas - Hukumar Kwastam ta Zone A ta sanar da kama buhunan shinkafa 7,259 na kasar waje mai nauyin kilogiram 50, kwatankwacin manyan motoci tireka 12 a watan Afrilun 2022.

Hukumar ta ce, rundunar ta kama wasu mutane 12 da ake zargi da shigo da haramtattacciyar shinkafar da sauran kayayyaki.

Kwastam ta yi babban kamu, ta kama tirelolin shinkafar waje mai guba
Kwastam ta kama manyan motoci 12 dauke da buhunan shinkafar waje mai guba | Hoto: thenationonlineng.net

Da yake zantawa da manema labarai a sashin a ranar Alhamis, 5 ga Afrilu, 2022, Kwanturolan Hukumar Kwastam mai kula da sashin, Hussein Ejebunu ya bayyana cewa an gano buhunan shinkafar da ba su dace da cin dan Adam ba.

Kara karanta wannan

Lauya ya kwashe kudin dake akawunt din dan sanda bayan ya mutu, EFCC ta damkeshi

An kama wadanda ake zargi da shigo da shinkafa mai guba da sauran kayayyaki

A cewar Ejebunu, an kama mutane 12 da ake zargi da aikata wasu laifuka daban-daban da suka saba da ka'idojin kwastam.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahoton Punch ya bayyana cewa Ejebunu ya ce bisa tsarin gwamnatin Najeriya na karfafa noman shinkafa, sashin ya kama buhuna 7,256 na shinkafa mai nauyin kilogiram 50 wanda zai cika manyan motoci tirela 12.

Shinkafar na kunshe da abubuwa masu hadari

Ya ce binciken dakin gwaje-gwaje na NAFDAC ya tabbatar da cewa shinkafar tana da illa kuma tana dauke da wasu sinadarai masu guba da bai kamata dan Adam ya ci ba, kamar yadda ta ruwaito.

Ejebunu ya gargadi ‘yan Najeriya da su lura da wasu buhunan shinkafa da ake shigowa da su na kasashen waje, yana mai cewa ba su da lafiya ga cimar dan Adam.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Shugaba Buhari ya bada umurnin bude bodar Jibiya da wasu guda 3

A wani labarin, hukumar kwastam ta sanar da cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin bude karin iyakoki guda hudu.

Iyakokin sun hada da Idiroko dake Ogun, Jibiya dake Katsina, Kamba dake Kebbi da Ikom dake Cross River.

Hukumar ya bayyana haka a sanarwa mai dauke da ranar wata 22 ga Afrilu, 2022 da E.I. Edorhe, mataimakin kwantrolan kwastam ya rattafa hannu, rahoton TheCable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel