Hotunan kafin aure: Diyar Sule Lamido na jhar Jigawa, zata yi wuff da kwamishina a Zamfara

Hotunan kafin aure: Diyar Sule Lamido na jhar Jigawa, zata yi wuff da kwamishina a Zamfara

  • Zukekiyar diyar tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigon jam'iyyar PDP, Sule Lamido, Surayya Lamido zata amarce
  • Za ta yi wuff da kyakyawan angonta Yazid Shehu Fulani 'dan asalin jihar Zamfara kuma an fara shirin bikin
  • Yazid a halin yanzu shine Turakin Zamfara kuma kwamishinan kasuwanci na jihar karkashin mulkin gwamna Matawalle

Surayya Sule Lamido, diyar tsohon gwamnan jihar Katsina, Sule Lamido, zata amarce da rabin ranta, Yazid Shehu Fulani.

Yazid Shehu Fulani shi ne Turakin Zamfara kuma kwamishinan kasuwanci mai ci a yanzu na gwamnatin jihar Zamfara.

Siratta da Yazid
Hotunan kafin aure: Diyar Sule Lamido na jhar Jigawa, zata yi wuff da kwamishina a Zamfara. Hoto daga @fashionseriesng
Asali: Instagram

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kyawawan hotunan zukekiyar amaryar tare da kyakyawan angonta sun bayyana inda shafin @fashoinseriesng suka bayyana cewa shirin biki ya kankama kuma yana gabatowa.

Kara karanta wannan

Ganduje zai cika alkawari, zai rattaba hannu domin rataye wanda ya kashe Hanifa

A hotunan da suka bayyana, an ga kyakyawar budurwa Surayya sanye da doguwar riga mai launin hoda inda ta waiwaya cike da murmushi ta kalla angonta Yazid wanda hankalinsa da tunaninsa baki daya ke kan rabin ransa.

Ta kara da kalmashe hannayenta a gaba yayin da angon nata ya rike daya daga cikin hannun amaryarsa cike da shaukin kauna.

Ga dai hotunan ku kashe kwarkwatar idanuwa:

Bidiyoyi da hotuna: An girgije a liyafar kammala shagalin auren Fatima Shettima da Sadiq Bunu

A wani labari na daban, a ranar Lahadi da ta gabata ne aka yi liyafar cin abincin dare ta kammala bidiri da shagalin auren diyar mataimakin 'dan takarar shugaban kasan Najeriya na jam'iyyar APC, Kashim Shettima, Fatima Shettima da angonta Sadiq Bunu.

Kamar yadda kayatattun hotuna da bidiyoyi suka bayyana, an ga angon da amaryarsa cike da natsuwa cikin shiga ta kamala da alfarma.

Kara karanta wannan

Sabbin Hotunan Gwamnan Jihar Neja Yana Tuka Babur Sun Bayyana

A cikin bidiyoyin da @fashionseriesng suka wallafa a shafinsu na Instagram, an ga amarya da angon cikin shigar kaya farare gwanin sha'awa.

Ba su kadai ba, abokai, kawaye da 'yan uwa sun taya ma'auratan murna yayin da suke kokarin shiga sabuwar rayuwa ta aure da ibada.

Asali: Legit.ng

Online view pixel