Yanzu-Yanzu: Hoton Osinbajo Na Farko Bayan Masa Tiyata Ya Bayyana

Yanzu-Yanzu: Hoton Osinbajo Na Farko Bayan Masa Tiyata Ya Bayyana

  • Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya wallafa hotonsa na farko bayan an masa tiyata a asibtin Legas
  • A hoton da ya wallafa a shafukansa na dandalin sada zumunta, an ga mataimakin shugaban kasar yana murmushi rike da sanda na taimaka masa yin tafiya
  • Matansa, iyalansa, abokai da likitan mataimakin shugaban kasar suna tare da shi a hoton da ya dauka

Jihar Legas - Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, SAN, ya wallafa hotonsa na farko kwanaki bayan an masa tiyata a cinyarsa a asibitin Duchess da ke Ikeja, Legas.

Yemi Osinbajo.
Yanzu-Yanzu: Hoton Osinbajo Na Farko Bayan An Masa Tiyata Ya Bayyana. Hoto: Aso Rock Villa.
Asali: Facebook

Cikin wani gajeren rubutu da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Osinbajo ya rubuta:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

"Bisa Tsautsayi Na Zama Shugaban Najeriya", In Ji Tsohon Shugaban Kasa Obasanjo

"Ina matukar godiya ga kowa da kowa saboda fatan alheri da addu'a bayan tiyata da aka yi min.
"Kuma godiya na musamman ga tawagar masu tiyata, likitoci, ma'aikatan jinya, kwararru bangaren motsa jiki da mahukunta na asibitin Duchess International Hospital Lagos, saboda bata kula mai inganci.
"Allah ya muku albarka baki daya."

Asali: Legit.ng

Online view pixel