Gaskiya Tayi Halinta: Yadda Aka Tirsasa CJN Tanko Yayi Murabus Kan Dole

Gaskiya Tayi Halinta: Yadda Aka Tirsasa CJN Tanko Yayi Murabus Kan Dole

  • Akasin abinda aka bayyana na cewa tsohon CJN Tanko da kansa yayi murabus, an gano cewa tirsashi aka yi ya saka hannu a kan takardar barin aiki
  • Bayanai sun tabbatar da cewa, a daren Lahadi aka je har gida aka dauke shi tare da tafiya da shi wani wurin kuma aka bashi takardar aka ce yasa hannu bisa umarnin Buhari
  • Wasu manyan jami'an gwamnati tare da wani babban shugaban hukumar tsaro ne ke da hannu wurin shirya lamarin wanda aka dauka shekara daya ana kullawa da kwancewa

FCT, Abuja - Murabus din alkalan alkalan Najeriya, Mai shari'a Ibrahim Tanko Muhammad a ranar Litinin ya biyo bayan wasu manyan fadi-tashi da aka dade ana shiryawa amma aka kaddamar da su a daren Lahadi, majiyoyi da dama da suka san kan lamarin suka tabbatar wa da Daily Trust.

Kara karanta wannan

Cikakken jerin Sanatoci 58 da aka zazzage, ba za su koma kujerunsu a Majalisar Dattawa ba

Majiyoyi masu karfi sun ce akasin tunanin da ake na cewa Muhammad yayi murabus da kansa ne, tirsasa shi aka yi daga cikin manyan jami'an tsaro da jami'an gwamnati.

Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya Muhammad Tanko
Gaskiya Tayi Halinta: Yadda Aka Tirsasa CJN Tanko Yayi Murabus Kan Dole. Hoto daga @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Bayan murabus dinsa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Mai Shari'a Olukayode Ariwoola, na biyu a daraja a kotun kolin, a matsayin mukaddashi alkalin alkalan Najeriya.

Yadda aka tirsasa CJN yayi murabus

Alamu sun fara nunawa akwai wata a kasa tun a safiyar Litinin da tsohon CJN bai halarci bude taron horar da alkali ba a NJI dake Abuja.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Muhammad bai bayyana a taron ba, bai aike dalilinsa ba kuma bai aika wakili ba.

Hadimansa sun ce basu san da batun murabus dinsa ba har sai safiyar Litinin.

Sai dai, wasu majiyoyi sun yi ikirarin cewa an umarcesa da ya bayyana a fadar shugaban kasa inda aka mika masa takardar murabus kuma aka ce ya saka hannu.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 10 da ya kamata ku sani game da tsohon shugaban alkalan Najeriya Tanko Muhammad

Daily Trust ta tattaro cewa, an dade ana shirin yadda za a sauke Muhammad kuma wani na gaba a fadar shugaban kasa da wani shugaban hukumar tsaro ne suke kan gaba. Sun hada da manyan jami'an majalisar zartarwa ta shari'a a shirin su.

Wata majiya a NJC tace an so aiwatar da lamarin shekarar da ta gabata amma aka dakatar da shi har zuwa ritayar Mai shari'a Mary Odili wacce za ta iya maye kujerarsa na kasa da shekara daya da ace Muhammad yayi murabus kafin ta tafi.

An alakanta batun murabus din da halin rashin lafiyar da yake ciki.

Wani SAN wanda ya bukaci a boye sunansa, yace an tirsasa tsohon CJN yayi murabus ne akan abubuwa biyu. Na farko kan wasikar da alkalai 14 suka aike masa da ita da kuma wata harkallar kudade.

Yace akwai batun rashin lafiya wanda an dade da sani amma aka bar CJN din ya cigaba da rike kujerar har zuwa watan Disamban 2023 da zai yi tiraya.

Kara karanta wannan

Rashawa? Dalilai masu karfi guda 5 da suka sa shugaban alkalai ya ajiye aikinsa

An cimma manufa a dare daya

Wata majiya makusanciya da tsohon CJN wacce ta bukaci a boye sunansa, tace an dauka Muhammad daga gidansa a daren Lahadi zuwa wani wuri wanda ba a sani ba.

"Daga isar sa, an mika masa takardar yasa hannu. An sanar da shi cewa daga shugaban kasa take kuma yayi biyayya saboda jin hakan. Ba a bashi damar tuntubar kowa ba har da iyalansa kafin ya sanya hannu," yace.

Amma wata majiya a kotun koli tace Muhammad na fama da matsalar rashin lafiya wacce take hana shi ayyukan yau da kullum har da zama yin shari'a da aiki kan takardun shari'a.

Yace lamarin yana daga cikin abinda ya kawo hargitsi a kotun wanda ya kai ga alkalai 14 sun aike masa da wannan wasikar.

"A watan Ramadan da ya gabata, shugaban kasa ya gayyaci mambobin shari'a zuwa fadarsa domin buda baki amma Muhammad ya shirya zuwa Kaduna a wannan lokacin. Da aka tunatar da shi, sai yace bai san da batun ba duk da an sanar da shi," majiyar tace.

Kara karanta wannan

Hadimin alkali: Babban dalilin da yasa shugaban alkalan Najeriya ya yi murabus

Buhari ya Gwangwaje Tsohon CJN Tanko da Lambar Yabo Mafi Daraja ta 2 a Najeriya

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya gwangwaje tsohon shugaban alkalan Najeriya, Muhammad Tanko da lambar yabo Grand Commander of the Order of Niger, GCON.

Lambar yabon ita ce mafi daraja ta biyu a lambobin karramawa da za a iya bai wa 'dan kasar Najeriya, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel