Yan bindiga sun kashe wani malamin addini a jihar Kaduna

Yan bindiga sun kashe wani malamin addini a jihar Kaduna

  • Tsagerun yan bindiga sun halaka wani malamin darikar Katolika, Rev. Fr. Vitus Borogo, a jihar Kaduna
  • Lamarin ya afku ne a lokacin da yan bindigar suka farmaki wani gona a hanyar Kaduna-Kachia a ranar Asabar, 25 ga watan Yuni
  • Shugaban darikar Katolika a jihar Kaduna, Rev. Fr. Christian Emmanuel, ya tabbatar da faruwa lamarin inda ya ce za a sanar da lokacin jana’izarsa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Wasu yan bindiga sun kashe babban malamin darikar Katolika na kwalejin fasaha ta jihar Kaduna, Rev. Fr. Vitus Borogo a ranar Asabar, 25 ga watan Yuni, a gonarsa da ke hanyar Kaduna-Kachia.

Shugaban darikar Katolika a jihar Kaduna, Rev. Fr. Christian Emmanuel, ya tabbatar da faruwa lamarin a wata sanarwa da aka gabatarwa kamfanin dillancin labaran Najeriya a Kaduna.

Jihar Kaduna
Yan bindiga sun kashe wani malamin addini a jihar Kaduna Hoto: The Nation
Asali: Facebook

Emmanuel ya ce an kashe Marigayi Borogo a gonar gidan yari, Kujama, hanyar Kaduna zuwa Kachia, bayan wasu da ake zaton yan ta’adda ne sun farmaki gonar, jaridar The Guardian ta rahoto.

Kara karanta wannan

Uwargidar Najeriyar gobe: Labarin Matan Tinubu, Atiku, Peter Obi da na Kwankwaso

Ya ce:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Fr Borogo na da shekaru 50 kuma shine babban malamin darikar Katolika na kwalejin fasaha ta jihar Kaduna, kuma shugaban kungiyar limaman Katolika na Najeriya (NCDPA), reshen Kaduna.
“Babban limamin Katolika Matthew Man-Oso Ndagoso, na Kaduna ya mika ta’aziyya ga iyalai, ahlin NFCS na kwalejin fasaha ta Kaduna da daukacin al’ummar kwalejin Kaduna sannan ya basu tabbacin kusantarsu da saka su a addu’a."

Ya ce nan ba da dadewa ba za a sanar da tsare-tsaren yadda jana’izarsa za ta kasance, jaridar The Nation ta rahoto.

Da aka tuntubi Kakakin yan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige kan lamarin, ya ce zai bincika sannan ya yi karin jawabi.

Yan Bindiga Sun Kashe Yan Bijilante Da Mafarauta 5 Da Suka Tafi Daji Don Ceto Manoma 22 Da Aka Sace a Niger

Kara karanta wannan

Kotu ta Bada Umarnin Kwace Kadarar Ɗan Sambo Dasuki Dake Abuja

A wani labarin, mun ji cewa yan bindiga sun harbe yan bijilante biyar har lahira da wani mafarauci daya a wani harin kwantar bauna da suka kai musu a dajin Lafiya-Kpada-Duma a Jihar Niger.

Daily Trust ta gano cewa wasu yan bijilante shida sun tsira da raunin bindiga sakamakon harin.

Wani dan bijilante wanda ke cikin tawagar wanda ya nemi a boye sunansa ya ce lamarin ya faru ne a ranar Juma'a bayan an gayyato yan bijilante daga Abuja da Niger don ceto wasu manoma 22 da aka sace a gona a kauyen Rafin-Daji a karamar hukumar Abaji na FCT, a ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel