Katsina: Rundunar Yan Sanda Ta Karrama Jami'inta Da Dawo Da Makuden Daloli Da Ya Tsinta a Sansanin Alhazai

Katsina: Rundunar Yan Sanda Ta Karrama Jami'inta Da Dawo Da Makuden Daloli Da Ya Tsinta a Sansanin Alhazai

  • Rundunar yan sandan Najeriya ta karrama wani jami'inta da ya tsinci makuden kudi a sansanin alhazai ya mayarwa mai shi
  • Nura Mande, ya samu takardar yaba hali daga Kwamishinan yan sanda Jihar Katsina da kuma tukwicin N30,000 saboda gaskiyarsa da amana
  • Kwamishinan yan sandan Jihar Katsina, Idris Dabban ya yi kira ga sauran yan sanda su yi koyi da irin halayen gaskiya da amana da Mande ya nuna

Katsina - Rundunar Yan Sandan Najeriya reshen Jihar Katsina ta karrama wani jami'inta mai mukamin Constable, Nura Mande, wanda ya tsinci dalla 800 ya kuma mayarwa mai shi a Katsina.

Sanawar da kakakin yan sandan Jihar, SP Gambo Isah ya fitar ta ce an bawa constable din wasikar yaba hali da N30,000 daga Kwamishinan yan sandan Jihar, Idris Dabban, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kwato Wasu Motocci Da Aka Sace Daga Najeriya Aka Kai Su Jamhuriyar Nijar

Gambo Isah and Nura Mande.
Katsina: Rundunar Yan Sanda Ta Karrama Jami'inta Da Dawo Da Makuden Daloli Da Ya Tsinta a Sansanin Alhazai. Hoto: @daily_trust.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yadda lamarin ya faru

Ya bayyana cewa Mande na aiki ne a Hukumar Jin Dadin Alhazai lokacin da ya tsinci dalla 800 mallakar wata maniyaciyya, Hajiya Hadiza Usman.

"Yayin da ya ke aikinsa a sansanin mahajjata, PC Mande ya tsinci $800 a kasa ya kuma mayarwa Direkatan Hukumar Alhazai, Alhaji Sada Salisu Rumah.
"PC Mande ya bayyana cewa tsoron Allah ne yasa ya mayarwa hukumar alhazai kudin domin a mayarwa mai shi.
"Salisu Rumah ya yaba wa dan sandan saboda halin gaskiya da amana," ya kara da cewa.

A cewar Isah, kwamishinan yan sanda ya ji dadin gaskiyar da Mande ya nuna ya kuma yi kira da sauran yan sanda su yi koyi da shi.

Ya bada tabbacin cewa rundunar za ta cigaba da yaba wa jami'anta da ke nuna gaskiya da amana wurin aikinsu, NAN ta rahoto.

Kara karanta wannan

Za a shirya wasan kwaikwayo a kan tarihin tsige Sanusi I da Sanusi II a 1963 da 2020

Sanatan APC Ya Saka Wa Daliget Da Kujerun Hajji Bayan Sun Dawo Masa Da Kudinsa Don Ba Su Zabe Shi Ba

A wani rahoton, Sanata Smart Adeyemi wanda ya wakilci Kogi West a Majalisar Tarayya, ya bada kujerun Hajji ga mutum biyar cikin daligets din da ya bawa kudi amma ba su zabe shi ba a zaben fidda gwani na APC.

Adeyemi ya rasa damar komawa majalisar ne a yayin da ya samu kuri'u 43 a zaben fidda gwanin, hakan yasa ya zo na uku.

Sunday Karimi, wanda ya samu tikitin jam'iyyar ya samu kuri'u 288, yayin da Muyiwa Aina wanda ya zo na biyu ya samu kuri'u 73.

Asali: Legit.ng

Online view pixel