Yan bindiga sun sace mutane da yawa, sun kona motoci a wani kazamin hari da suka kai babbar hanyar Kaduna

Yan bindiga sun sace mutane da yawa, sun kona motoci a wani kazamin hari da suka kai babbar hanyar Kaduna

  • Tsagerun yan bindiga sun farmaki babbar hanyar Kaduna-Birnin Gwari inda suka yi garkuwa da matafiya masu yawan gaske
  • An tattaro cewa yawancin wadanda maharan suka sace mata ne da kananan yara, sun kuma kona motoci takwas a yayin harin
  • Zuwa yanzu babu sanarwa daga rundunar yan sandan jihar Kaduna ko gwamnatin jihar da ke tabbatar da wannan lamari

Kaduna - Rahotanni sun kawo cewa tsagerun yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama bayan sun farmaki matafiya a hanyar babban titin Kaduna-Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.

Majiyoyi sun bayyana cewa yan bindigar sun toshe babbar hanyar a ranar Talata, 31 ga watan Mayu, sannan a cikin haka suka kona motoci takwas, Channels Tv ta rahoto.

An tattaro cewa bayan nan maharan sun yi awon gaba da wasu adadi na matafiya wanda mafi yawansu mata da yara ne zuwa wani waje da ba a sani ba.

Kara karanta wannan

'Yan Sanda Sun Kai Samame Maɓuyar Masu Garkuwa, Sun Ragargajesu Sun Ceto Mutane

Yan bindiga sun sace mutane da yawa, sun kona motoci a wani kazami hari da suka kai babbar hanyar Kaduna
Yan bindiga sun sace mutane da yawa, sun kona motoci a wani kazami hari da suka kai babbar hanyar Kaduna Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Koda dai hukumomin yan sanda a jihar basu riga sun tabbatar da lamarin ba, babu tabbacin ko an rasa rai a harin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar masu tabbatar da tsaro da shugabanci nagari a Birnin Gwari, Ibrahim Nagwari, ya tabbatar da harin a cikin wata sanarwa da ya fitar.

A yawabinsa, ya bayyana cewa yan bindiga sun toshe babbar hanyar Birnin Gwari-Kaduna sannan suka kama ayarin masu motoci tare da rakiyar tsaro tsakanin Kuriga da Manini, kusa da Udawa inda suka tsere da wasu adadi na mutane zuwa cikin jeji.

Nagwari wanda ya nuna tsoron cewa mayakan sun hade da mayakan Ansaru don yakar mazauna garin Birnin Gwari ya ci gaba da cewar har yanzu alkawarin siyasa da gwamnati ta dauka na magance matsalar tsaro ya ci tura.

Ya shawarci mutane da su daina bi ta babbar hanyar Kaduna Birnin Gwari har sai lamarin tsaro ya inganta a wajen.

Kara karanta wannan

Yadda aka tsinci gawarwakin wani dan kasuwa, matarsa da yaransu 3 baje a gidansu

Ya ce:

“A kodayaushe muna yaba kokarin jami’an tsaro a kokarinsu na dakile matsalolin tsaro da ke addabar yankin Birnin Gwari gaba daya, amma tura ta kai bango.
“Akwai bukatar mutanen Birnin Gwari da garuruwan da ke hanyar Kaduna-Birnin Gwari su gaggauta daina bi ta hanyar mai mummunar hatsari har sai lamuran tsaro sun inganta.”
“Saboda haka wannan kungiya tana shawartan dukkanin al’ummarmu da su dan janye sannan su bi dukkanin dokokin kasarmu sannan su dage da addu’a don Allah ya shiga lamarin tare da yin maganin wadannan yan ta’adda da abokan huldarsu a cikin garuruwanmu.
“Hakazalika, muna addu’ar Allah ya dawo mana da mutanenmu, galibi mata da kananan yara da aka sace.”

Jaridar Punch ta rahoto cewa jami’in hulda da jama’a na kungiyar masu ci gaban masarautar Birnin Gwari, Idris Sa’idu, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ‘yan bindigar sun yi wa wasu wurare uku kawanya a kan babbar hanyar inda suka tilasta wa masu ababen hawa juyawa.

Kara karanta wannan

Miyagun Yan bindiga kan 'Babura sama da 200' sun kai wani mummunan hari jihar Katsina

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun halaka tsohon kwamishinan NPC, sun sace 'ya'yansa mata

A wani labarin, wasu miyagun yan bindiga sun kashe tsohon kwamishinan hukumar ƙidaya ta ƙasa (NPC), Zakari Umaru-Kigbu, a jihar Nasarawa, kuma suka sace ƴaƴansa mata biyu.

Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru bayan rabawar daren da ya gabata a gidansa da ke Azuba Bashayi, ƙaramar hukumar Lafiya jihar Nasarawa.

Haka nan kuma wasu bayanai sun nuna cewa maharan sun bukaci a tara musu miliyan N50m a matsayin kuɗin fansar waɗan da suka sace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel