"Zai yi wahala a ga watan Shawwal a ranar Asabar, watakila bikin Sallah sai Litinin"

"Zai yi wahala a ga watan Shawwal a ranar Asabar, watakila bikin Sallah sai Litinin"

  • Simwal Usman Jibril ya yi bayani game da lokacin da za a haifi watan Shawwal na shekarar 1443
  • Masanin yana cikin 'yan kwamitin da ke kula da harkar ganin wata a majalisar NSCIA ta Najeriya
  • A cewar Simwal Jibril, ana la’akari ne da zahirin ganin wata wajen yanke hukunci ba kimiyya ba

Nigeria - Simwal Usman Jibril yana cikin majalisar da ke kula da sha’anin ganin wata a Najeriya, ya yi bayani a game da haihuwar watan Shawwal.

A wata hira da BBC Hausa ta yi wa da Malam Simwal Usman Jibril a ranar Asabar, ya nuna zai yi wahala a ga jinjirin watan sallah a yammacin yau.

Wannan kwamiti ya na karkashin majalisar koli na harkokin addinin musulunci wanda Mai alfarma Sarkin Musulmi ke jagorantar ayyukanta.

Kara karanta wannan

Wata za ta riga rana fadi ranar Asabar amma duk da haka a fita duban wata, kwamitin duban wata

Masanin ya fara da cewa kwamitinsu ya na dogara ne da ganin wata a zahiri kamar yadda addini ya koyar, ya ce ba da lissafin taurari su ke amfani ba.

A tattaunawarsa da ‘yan jarida, ‘dan kwamitin ganin watan ya yi bayani daga Kur’ani kan yadda Ubangiji ya ba ‘Dan Adam ilmin sanin tafiyar wata.

Kafin a haifi sabon jinjirin wata a Duniya, masanin ya ce lissafi ya nuna ana daukar kwanaki 29.53.

Shawwal
Jinjirin wata ya girma Hoto: unsplash.com
Asali: UGC

A lokaci daya ne ake haihuwar sabon wata a duk fadin Duniya. Sai dai kuma kasashe su na samun ganin jinjirin watan ne a lokuta mabanbanta da maraice.

Duk da cewa a yammacin yau ne za a zura ido domin neman watan Shawwal, Amma idan aka koma batun ilmin kimiyya, da kamar wuya ya bayyana.

Kara karanta wannan

Eid al Fitr: Hukumomin kasar Saudiyya sun sanar da ranar da za fara duban jinjirin watan sallah

Aikin kwamitin ganin wata shi ne tantance rahotannin da suke samu daga jama’a. Bayan nan kuma sai su sanar da fadar Sultan, Alhaji Sa’ad Abubakar III.

Simwal Jibril ya ce a lokacin da za a gama haihuwar watan gobe a yau, sai kusan karfe 11:28 a kasar Saudi, a Najeriya kuma karfe 9:28 na dare kenan.

“Haihuwar sabon watan Shawwal zai faru ne a yau (Asabar), 30 ga watan Afrilu 2022 da kafe 9:28 na dare a Najeriya.”

“A wannan mataki, idan wannan ya faru to daga nan ne ake iya ganin jinjirin wata. Za a haifi wata bayan faduwar rana.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel