Yanzu-Yanzu: Dillalan man fetur sun zauna, sun amince a magance karancin man fetur

Yanzu-Yanzu: Dillalan man fetur sun zauna, sun amince a magance karancin man fetur

  • Dillalai da masu dauko man fetur sun gana a ABuja, sun fitar da mafita kan yadda man fetur zai wadata
  • Sun sanya hannu kan wata yarjejeniya da za ta tabbatar da isar da man fetur dukkan sassan kasar nan
  • Sun yi haka ne a cewarsu domin dakile karancin mai da ke addabar 'yan Najeriya a wannan shekara da muke ciki

Abuja - Kungiyar Masu Sufurin Man Fetur (ADITOP) da Kungiyar Dillalan Man Fetur ta Najeriya (IPMAN) sun rattaba hannu kan wata yarjejeniya domin tabbatar da samar da man fetur a fadin kasar nan.

Shugabannin ADITOP da IPMAN, Alhaji Lawan Dansaki da Dattijo Chinedu Okoronkwo ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Abuja, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Allah wadai: Martanin Atiku, Saraki, Shehu Shehu kan harin jirgin kasan Kaduna

Tsadar mai a Najeriya
Yanzu-Yanzu: Dillan man fetur sun zauna, sun amince a magance karancin man fetur | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Da yake zantawa da manema labarai, Okoronkwo ya bayyana fatansa na cewa hadin gwiwa da ADITOP, wanda mambobinsa masu manyan motocin dakon man fetur ne, zai rage wa ‘yan Najeriya radadin wahalar da suke sha wajen samun mai a kasar

A cewarsa:

“Manyan gidajen mai da tankunan da kuke gani a fadin kasar nan, hadin gwiwa ne na ADITOP da IPMAN.
"Mun yi imanin cewa wannan hadin gwiwar zai tabbatar da cewa man fetur sun isa kowane lungu na Najeriya."

Ya kuma ce yarjejeniyar za ta kawo karshen yajin aikin da ake yi a bangaren mai da iskar gas.

Shugaban ADITOP, Dansaki, ya jaddada cewa hadin gwiwa ta zama wajibi don magance duk wani cikas wajen isar da man fetur kasar.

A kalamansa:

“Su ne suka mallaki gidajen mai, mu kuma mun mallaki manyan motoci. Hadin gwiwar za tq taimaka mana kuma ta taimaka musu don tabbatar da cewa an kai duk kayayyakinsu su zuwa tashoshin su.

Kara karanta wannan

Muna alfahari: Gwamnatin Buhari ta ji dadin yadda 'yan Najeriya ke more tafiya a jirgin kasa

“Kafin yanzu, muna yin haka ne a ware. Suna yin nasu, mu ma mu kan yi namu, amma yanzu da wannan rikicin na karancin man fetur, mun ga ya dace mu hada kai."

Najeriya na da mai sama da lita 1.9bn a boye, ministan Buhari

Timipre Sylva, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur ya bayyana cewa yanzu haka Najeriya na da lita biliyan 1.9 na man fetur a ajiye.

A cewarsa, wannan mai na iya gamsar da bukatun kasar na tsawon kwanaki 32, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Ministan ya bayyana haka ne jiya Laraba 9 ga watan Maris a Abuja yayin da yake magana a gaban majalisar zartarwa ta tarayya a zaman da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Babban Manajin Darakta na Kamfanin Mai na Najeriya Mista Mele Kyari ya raka shi a taron na FEC da aka yi.

Najeriya ta sayar da danyen mai na N14.4trn a 2021 ga wasu kasashe 5

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Ma'aikatan jami'a karkashin SSANU da NASU sun hargitsa jami'ar Legas

A wani labarin, Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana cewa Najeriya a 2021 ta samu sama da Naira tiriliyan 14.4 na kudin danyen mai daga kasashe daban-daban na duniya.

NBS ta bayyana hakan ne a cikin sabon rahotonta na kididdigar cinikayyar kasashen waje da aka buga a shafinta na yanar gizo a ranar Talata, 15 ga Maris, 2021.

Bisa kididdigar da aka yi, an ce cinikin danyen mai ya kai aU 76.22 na jimillar fitar da man da aka yi a cikin shekarar da aka yi nazari a kai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel