Yadda titin Ohanmi a jihar Edo ya koma bayan wata guda kacal da kammalawa, BudgIT

Yadda titin Ohanmi a jihar Edo ya koma bayan wata guda kacal da kammalawa, BudgIT

  • Hotunan wani titin da ya lalace wata daya bayan kammala shi ya bayyana a kafafen sada zumunta
  • Kungiyar BugdIT ta bayyana cewa ma'aikatar noma aka baiwa kwangilan gina titin amma bata bibiya ba
  • BudgIT wata kungiyar fafutuka ce mai amfani da ilmin zamani wajen bibiyar ayyukan da gwamnati ke yi

Kungiyar BugdIT ta yi kira ga majalisar dokokin tarayya ta sake dubi cikin kasafin kudin Najeriya saboda an bada kudaden wasu ayyuka amma ba'ayi yisu yadda ya kamata.

BudgIT ta saki hotunan wani titi da aka kammala wata guda yanzu amma duk ya lalace.

A jawabinta, ta yi alhinin Titin Ohanmi Road a karamar hukumar Owan East ta jihar Edo bayan wata guda da budeta.

Tace:

Kara karanta wannan

Hotunan Firdawsi Bayero, Gimbiyar Kanon da Sarkin Iwo zai aura yau sun bayyana

"Titin Ohanmi Road a karamar hukumar Owan East ta jihar Edo da aka baiwa ma'aikatar noma a 2021."
"Haka titin ya koma bayan wata daya da ginashi saboda gazawar ma'aikatar wajen bibiyan kwangilan da kuma gazawar mai kwangilan."
"Muna kira ga majalisar dokokin tarayya ta sake duba kasafin kudi."

BudgIT
Yadda titin Ohanmi a jihar Edo ya koma bayan wata guda kacal da kammalawa, BudgIT Hoto: BudgIT
Asali: Facebook

Titin Ohanmi
Yadda titin Ohanmi a jihar Edo ya koma bayan wata guda kacal da kammalawa, BudgIT Hoto: BudgIT
Asali: Facebook

BudgIT wata kungiyar fafutuka ce mai amfani da ilmin zamani wajen bibiyar ayyukan da gwamnati ke yi da tsare-tsarenta don sanar da yan kasa abinda ke faruwa.

Oluseun Onigbinde da Joseph Agunbiade ne suka kafata a 2011 a Legas.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel