Kotu ta jefa lauyan bogin da yaje ofishin EFCC karban belin wani kurkukun shekara daya

Kotu ta jefa lauyan bogin da yaje ofishin EFCC karban belin wani kurkukun shekara daya

  • Wata kotu ta musamman dake jihar Legas ta jefa lauyan bogi gidan gyara hali na tsawon shekara guda
  • An damke lauyan ne a watan Junairu lokacin da yaje ofishin EFCC karban belin wani madamfari
  • Alkalin kotu ta ce wajibi ne ya sha daurin shekara guda kuma babu zabin tara

Legas - Kotu ta yanke hukuncin daurin shekara guda a gidan gyara hali ga lauyan bogin da ya je ofishin hukumar EFCC kwanakin baya karbar belin wani wanda ake tuhuma da almundahana.

Bayan damke shi, hukumar ta gurfanar da mutumin mai suna Emmanuel Adekeye Adekola a gaban kuliya a jihar Legas.

Bayan watanni biyu ana shari'a, Alkalin kotun ta yankewa mutumin daurin shekara guda a gidan gyara hali.

EFCC ta bayyana hakan a jawabin da ta saki ranar Laraba a shafinta na Facebok.

Kara karanta wannan

EFCC ta saki tsohon gwamna bayan kwashe kwana 6 a hannunta, ta kwace fasfotinsa

A cewarta:

"Mai shari’a Sherifat Solebo dake kotu ta musamman dake Legas ranar Laraba, 23 ga watan Maris, 2022, ta yanke ma Emmanuel Adekeye Adekola hukuncin zama gidan gyara halinka bayan hukumar EFCC ta gurfanar dashi akan laifi mai alaka da sojin gona.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya amsa laifukan da aka tuhume shi inda mai shari’ar ta yanke masa hukuncin shekara daya ba tare da zabin biyan tara ba."

Lauyan bogi
Kotu ta jefa lauyan bogin da yaje ofishin EFCC karban belin wani kurkukun shekara daya Hoto: EFCC
Asali: Facebook

Hukumar EFCC ta damke Lauyan bogi da yaje ofishinta karban belin wani madamfari

A watan Junairu, hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzkin kasa zagon kasa watau EFCC ta damke lauyan bogi, Adekola Adekeye, kan laifin kirkiran takardun bogi don damfara.

Kakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis a Abuja, rahoton NAN.

Kara karanta wannan

Dan ta'adda ya gudu daga hannun hukuma yayinda aka kaishi kotu

Ya ce asirin lauyan ya tonu ne lokacin da yaje ofishin hukumar karban belin wani dan damfara.

Sun je har gidansa don bincike

Uwujaren yace jami'an EFCC sun garzaya gidansa don gudanar da bincike kawai sai suka tarar takardun bogi na jami'ar jihar Legas.

"Yayinda aka gudanar da bincike gidansa, an gano takardun bogi na tun shekarar 2005," yace.
"Ya yi ikirarin cewa shine mai ofishin “A.A. Emmanuel & Co. Chambers”, da yake amfani wajen damfara kafin a damkeshi, Za'a gurfanar da shi a kotu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel