Bayan na jiya, wutar Najeriya ta sake lalacewa, Abuja, Legas, da wasu jihohin sun shafu

Bayan na jiya, wutar Najeriya ta sake lalacewa, Abuja, Legas, da wasu jihohin sun shafu

Wasu jihohin Najeriya a ranar Talata sun sake shiga cikin duhu sakamakon sake lalacewar tushen wutar lantarkin Najeriya.

Jami'an hulda da jama'a kuma kakakin kamfanin lantarkin Ikeja Disco, Mr Felix Ofulue, ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai NAN a Legas.

A cewarsa, sun samu labarin lalacewar wutar kuma sun jiran a gyara.

Bayan na jiya, wutar Najeriya ta sake lalacewa, Abuja, Legas, da wasu jihohin sun shafu
Bayan na jiya, wutar Najeriya ta sake lalacewa, Abuja, Legas, da wasu jihohin sun shafu
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Hakazalika Eko Electricity Distribution Company (EKEDC) ya tabbatar da irin hakan a wani jawabi.

Kamfanini sun bayyana cewa wutar ta lalace ne misalin karfe 5:10 na yamma.

Sun ce wannan lalacewar ta hana kawo wuta wa kwastamominsu.

Eko Disco tace:

"Ya ku kwastamominmu, muna masu sanar da ku cewa an samke samun matsala da tushen wutan lantarkin Najeriya misalin karfe 5:10 na yau (Talata)."

Kara karanta wannan

Idan PDP bata ci zaben 2023 ba zata iya mutuwa gaba daya, Atiku

"Muna dakon lamarin kuma zamu sanar da ku inda aka kwana."

Asali: Legit.ng

Online view pixel