Idan PDP bata ci zaben 2023 ba zata iya mutuwa gaba daya, Atiku

Idan PDP bata ci zaben 2023 ba zata iya mutuwa gaba daya, Atiku

Tsohon shugaban kasa, Atiku Abubakar ya gargadi mambobin majalisar dattawan jam'iyyar Peoples Democratic Party PDP cewa jam'iyyar na iya mutuwa idan bata ci zaben shugaban kasa a 2023 ba.

Atiku wanda ya bayyana hakan yayinda ya karbi bakuncin mambobin kwamitin amintattun PDP ya bukacesu su taimaka su bashi daman nasara a zaben 2023.

Idan PDP bata ci zaben 2023 ba zata iya mutuwa gaba daya, Atiku
Idan PDP bata ci zaben 2023 ba zata iya mutuwa gaba daya, Atiku
Asali: Depositphotos

Ya ce mulkinsa da Obasanjo tsakanin 1999 da 2007 ne mafi alkahri ga Najeriya har yanzu.

A cewarsa:

"Da yawa cikin gwamnatin PDP tsakanin 199 da 2007. Har ila yau, babu gwamnatin da ta samu nasarori irin namu."
"Abinda nike fadi gaskiya ne kuma ina da hujjoji, a harkar noma, a harkar ilimi."

Kara karanta wannan

Atiku ga manyan PDP: Don Allah ku kara bani dama na gwada takara a 2023 ko zan dace

"Ina tsoron kuma ya kamata kuji tsoron idan bamuy nasara ba, hakan na nufin zamu kasance yan adawa na karin shekaru takwas. Nan da shekaru 8 masu zuwa, ban san mutum nawa cikinmu zai kasance cikin siyasa ba ko tuni jam'iyyar ta mutu."
Saboda haka wannan lokaci na da muhimmanci ga tarihinmu da rayuwarmu."

Asali: Legit.ng

Online view pixel