Da Dumi-Dumi: Abokin harkallar ƙasurgumin mai garkuwa da mutane ya amsa laifinsa a gaban Kotu

Da Dumi-Dumi: Abokin harkallar ƙasurgumin mai garkuwa da mutane ya amsa laifinsa a gaban Kotu

  • Ɗaya daga cikin mutanen dake da alaƙa da kasurgumin mai garkuwa Evans ya canza jawabi a Kotu, ya amsa laifin da ake tuhumarsa
  • Mista Udeme ya amsa laifinsa a zaman Kotun na yau Jumu'a, kuma tuni Kotun ta yanke masa hukuncin zaman gidan kaso
  • Alkalin Kotun dake zamanta a Ikeja, Oluwatoyin Taiwo, ya yanke masa shekara 5 kuma ya ba da umarnin hukuncin ya soma tun sanda aka tsare shi

Lagos - Mista Frank Udeme Upong, ɗaya ɗaga cikin waɗan da ake tuhuma da haɗa hannu da kasurgumin mai garkuwa da mutane, Chukwudimeme Onwuamadike, wanda aka fi sani da Evans ya canza bayani a Kotu.

The Nation ta rahoto cewan Upong wanda a baya ya musanta tuhumar da ake masa, ya dawo ya amsa cewa ya aikata abin da ake zarginsu da shi.

Kara karanta wannan

Jirgin kasan Legas zuwa Ibadan ya tsaya tsakiyar daji saboda mai ya kare

Evans
Da Dumi-Dumi: Abokin harkallar ƙasurgumin mai garkuwa da mutane ya masa laifinsa a gaban Kotu Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

An gurfanar da Udeme Upong, Evans, Joseph Ikenna Emeka, da Chiemeka Arinze a gaban Kotun Ikeja bisa tuhumar kisan kai, yunkurin kisa, haɗa baki wajen garkuwa da kuma siyar da makamai.

Ana zargin mutanen da yunkurin yin garkuwa da shugaban kamfanin motoci 'Young Shall Grow Motors,' Vincent Obianodo.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A zaman Kotu da ya gabata, rahoto ya nuna cewa an sanar da mutuwar ɗaya daga cikin waɗan da ake zargi, Chiemeka Arinze, wanda ya mutu ranar 26 ga watan Nuwamba.

Yayin da aka cigaba da zaman shari'ar ranar Jumu'a, Mista Upong, ta bakin lauyan dake karesa, Mista A. B. Josiah, ya shaida wa Kotu nufinsa na canza bayani.

Wane mataki Kotu ta ɗauka?

Da yake yanke hukunci, Kotun ta yanke wa Mista Udeme hukuncin zaman gidan gyaran hali na tsawon shekara 5 bayan kama shi da laifin siyar da makamai.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Kotu ta ba gwamnan APC umarnin ci gaba da zamansa a ofis bayan umarnin tsige shi

Alƙalin Kotun mai shari'a Oluwatoyin Taiwo, ya yanke masa hukuncin ranar Jumu'a, biyo bayan amsa laifinsa da ya yi.

Alkalin ya ba da umarnin cewa hukuncin zai fara ne tun daga ranar da aka fara tsare shi bayan ya shiga hannu.

Premium Times ta rahoto alkalin Ya ce:

"Duba da amsa laifinsa da ya yi, ina mai yanke wa wanda ake zargi shekara 5 a gidan Yari, kuma hukuncin zai fara ne tun lokacin da aka tsare shi wato 16 ga watan Yuli, 2017."

A wani labarin na daban kuma yayin da APC ke fama da rikicin cikin gida, Gwamna Buni, Malami da gwamnan CBN sun dira Landan zasu sa labule da Buhari

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Mala Buni mai barin gado ya canza tunani, daga Dubai duba lafiya zai wuce Landan ya gana da Buhari.

Rahoto ya nuna cewa Buni zai gana da Buhari ne domin jin abinda ke faruwa daga bakinsa kan zancen tsige shi.

Kara karanta wannan

Indiya ta maye gurbin Najeriya matsayin hedkwatar talauci na duniya

Asali: Legit.ng

Online view pixel