Da dumi-dumi: Kotu ta ba gwamnan APC umarnin ci gaba da zamansa a ofis bayan umarnin tsige shi

Da dumi-dumi: Kotu ta ba gwamnan APC umarnin ci gaba da zamansa a ofis bayan umarnin tsige shi

  • Hankalin gwamna da mataimakinsa na jihar Ebonyi ya tashi yayin da kotu ta ba da umarnin a tsige su cikin gaggawa
  • Wannan na zuwa ne yayin da gwamnan da mataimakinsa suka sauya sheka daga jam'iyyar da aka zabe su PDP zuwa APC
  • Sun tafi kotu domin kalubalantar shari'ar, yau dai wata kotu ta ba da umarnin a basu damar ci gaba da zaman ofis na tsawon kwanaki bakwai

Ebonyi - Gwamna David Umahi na jihar Ebonyi da mataimakinsa Dr. Kelechi Igwe, sun samu umarnin wucin gadi daga wata babbar kotun jihar inda za su iya zama na tsawon kwanaki bakwai.

Umurnin ya bayyana cewa, gwamnan da mataimakinsa za su zauna daram a ofis kuma ba za a cire su daga mukamansu ba, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Karin bayani: PDP ta mika sunayen masu maye gurbin gwamnan APC da mataimakinsa da aka tsige ga INEC

Gwamnan Ebonyi da mataimakinsa da su ci gaba da zama a ofis
Da dumi-dumi: Kotu ta ba gwamnan APC umarnin ci gaba da zamansa a ofis bayan umarnin tsige shi | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Twitter

Mai shari’a Henry Njoku ne ya bayar da wannan umarni, wanda a ranar 28 ga Fabrairu, 2022, ya yanke hukunci kan Umahi a karar da dan takarar gwamna, Sen. Sonny Ogbuorji na jam’iyyar APC, a zaben 2019 ya shigar.

Hakazalika, Umahi da Igwe sun kuma bukaci wata babbar kotun tarayya da ta ba da umarnin dakatar da aiwatar da hukuncin da ta yanke na tsige su a makon jiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wanda PDP ta zaba ya maye gurbin Umahi ya magantu

A bangare guda, dan majalisar wakilai, Iduma Igariwey, ya bayyana cewa, ci gaba da zaman Umahi da mataimakinsa a ofis ya zaba doka, yana mai cewa yanzu shi tsohon gwamna ne, inji rahoton jaridar The Punch.

Igariwey, wanda jam’iyyar PDP ta tsayar domin maye gurbin Umahi bayan wata babbar kotun tarayya ta ba da umarnin tsige shi da mataimakinsa, ya bukaci INEC da ta aiwatar da hukuncin da kotun ta yanke tare da ayyana shi a matsayin gwamna.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta maida zazzafan martani kan tsige gwamnan Ebonyi da ya sauya sheka daga PDP

2023: Kamata Ya Yi PDP Ta Nemi Gafara Daga Yan Najeriya, Ba Kuri'unsu Ba, Lawan

A wani labarin, a ranar Alhamis Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce ya kamata babbar jam’iyyar adawa wato PDP ta zagaya kasa wurin neman yafiyar ‘yan Najeriya maimakon zagayen kamfen na neman kuri’u.

Lawan ya ce shekaru 16 da PDP ta yi tana mulki ta lalata kasa gaba daya, hakan yasa ya ce ya kamata ta nemi afuwa a wurin mutane ba kuru’un su ba,Vanguard ta ruwaito.

Kamar yadda Lawan ya ce, 2022 shekarar cin gajiyar mulkin APC ne inda za a kaddamar da ayyukan da shugabanni suka yi kafin karshen shekarar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel