Zamfara: A karon farko, mataimakin gwamna da majalisa ke yunkurin tsigewa ya yi martani

Zamfara: A karon farko, mataimakin gwamna da majalisa ke yunkurin tsigewa ya yi martani

  • Mahdi Ali Gusau, mataimakin gwamnan jihar Zamfara da majalisa ke kokarin tsigewa, ya ce ba za su iya cigaba da komai ba saboda lamarin na gaban kotu
  • A cewar Mahdi wanda lauya ne, duk dan majalisar da ya cigaba da yunkurin tsige shi toh babu shakka jahili ne kuma bai san abinda ya ke yi ba
  • Ya bayyana cewa, cikin girma da iko irin na Allah ne suka samu shugabanci ta hannun kotu amma a yau su ke take dokar kotu

Gusau, Zamfara - Mataimakin gwamnan jihar Zamfara, Mahadi Ali, ya yi magana a karon farko bayan da majalisar jihar ta fara yunkurin tsige shi inda ya ce 'yan majalisar ba za su iya cigaba da komai ba.

Kara karanta wannan

An tsaurara tsaro: Majalisar jiha na shirin tsige mataimakin kakaki bisa kin jinin APC

"Ba za su iya cigaba da kokarin tsige ni ba saboda maganar ta na gaban kotu," Ali Gusau ya ce a wani jawabi da yayi wa manema labarai a babban birnin jihar a yammacin Lahadi.

Premium Times ta ruwaito cewa, majalisar jihar Zamfara ta fara kokarin tsige mataimakin gwamnan jihar.

Zamfara: A karon farko, mataimakin gwamna da majalisa ke yunkurin tsigewa ya yi martani
Zamfara: A karon farko, mataimakin gwamna da majalisa ke yunkurin tsigewa ya yi martani. Hoto daga premiumtimesng.com
Asali: UGC

Idan suka cigaba kuma, jahilai ne

Ali a ranar Lahadi ya martani kan abinda ke faruwa da kakkausar murya. Ya ce dan 'yan majalisar za su yi abun marasa ilimi ne idan suka cigaba da kokarin tsige shi.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Na zo nan ne a yau domin tsokaci kan kokarin tsige ni da ke yi. Na ji cewa babban alkalin jihar ya kafa kwamiti domin bincika ta. Ta yaya za su cigaba da yunkurin? Ta yaya alkalin zai kafa kwamitin bayan ya san lamarin ya na gaban kotu?" Ali ya ce a harshen hausa.

Kara karanta wannan

Ganduje ga 'yan tsagin Shekaru: Kawai ku amince kun sha kaye, ku zo mu hada kai

Mataimakin gwamnan wanda lauya ne, ya ce ya sanar da 'yan majalisar cewa ba za su iya cigaba da kokarin tsige shi ba, Premium Times ta ruwaito.

"Amma hakan na nuna cewa su ba komai bane face jahilai. Idan suka cigaba da yunkurin hakan, jahilai ne kawai. Ya dace su san akwai iyaka a komai da suke yi.
“Kun ga abinda nake ta fada muku ko? Allah na da girma. Wannan gwamnatin ta samu mulki ne sakamakon hukuncin kotu kuma aka sanar da mu matsayin masu nasara bayan mun zama na biyu a zabe, a yanzu kuma ga mu muna take dokar kotun.
"Kotu ta bukaci kowanne bangare da ya jira har sai ta yanke hukunci kan lamarin amma sun yanke hukuncin cigaba da kokarin tsige ni," yace.

Yan majalisa 18 cikin 22 sun amince a tsige mataimakin gwamnan Zamfara, sun umurci Alkali ya fara bincike

A wani labari na daban, mutum 18 cikin 22 na mambobin majalisar dokokin jihar Zamfara sun amince da kudirin tsige mataimakin gwamnan jihar, Mahdi Aliyu Gusau.

Kara karanta wannan

Ku mika wuya tun kafin mu iso maɓoyarku, Sabon Kwamishina ya aike da sako ga yan bindiga

Wannan ya faru ne kwanaki uku bayan majalisar ta aike masa da sakon tuhume-tuhumen da ake masa.

A zaman ranar Alhamis, mambobin majalisa uku basu halarta ba, rahoton Ptimes. Dan majalisa na jam'iyyar PDP, Salihu Usman (Zurmi ya gabas), kadai ne wanda bai amince a tsige Mahdi Gusau ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng