Akwai yiwuwar gidajen mai su kara farashin fetur, lita za ta iya haura N180 a Najeriya
- Mafi yawan masu saidawa gidajen mai a manyan tassoshin kasar nan sun kara farashin litar fetur
- Ana saida kowace lita a kan akalla N162 a tashoshi, a wasu wurare a Kudu, har tsadar ta kai N180
- Idan masu gidajen mai sun saye fetur da tsada haka, ba zai yiwu a cigaba da saida lita a kan N165 ba
Nigeria - Farashin kowane litar PMS wanda aka fi sani da man fetur zai iya kai ko ma ya zarce N180 a mafi yawan gidajen mai nan da wasu ‘yan makonni.
Jaridar Punch ta kawo rahoto a ranar Litinin 21 ga watan Fubrairu 2022 cewa farashi zai tashi idan ba a dauki mataki a kan karin da aka samu a yanzu ba.

Kara karanta wannan
‘Yan bindiga sun ‘aure’ wasu yaran makarantar da aka gagara kubutarwa, sun yi masu ciki
A halin yanzu, ana ta kara farashin man fetur a manyan tashoshin ‘yan kasuwar da ke kasar nan.
Farashin lita a tashoshin mai ya tashi daga N142 zuwa N165 da aka saba saidawa a gidajen mai zuwa tsakanin N162 da N170 a ‘yan kwanakin bayan nan.
Hakan ta sa a wasu gidajen mai an ga canjin farashi daga N165 da gwamnatin tarayya ta kayyade zuwa N180. A wasu wuraren ma farashin lita ya zarce hakan.
Me hukumomi suke cewa?
Rahoton da jaridar ta fitar ya bayyana cewa NNPC ta ce ba ta san da karin da gidajen man ‘yan kasuwa suka yi ba. NNPC kadai yake shigo da tacaccen mai.

Asali: Getty Images
Haka zalika hukumar Nigeria Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority ta bukaci ‘yan kasuwa su sanar da su a kan wani sauyin farashi.
Mai magana da yawun bakin kungiyar ‘yan kasuwan mai a Najeriya ta IPMAN, Cif Ukadike Chinedu ya tabbatar da cewa ana saida lita ne a N170-N180.
Farashi ya yi zama - IPMAN
“’Yan kasuwa su na saida lita a kan N167 ko N170 a tashoshinsu. Wani aboki na ya tuntube ni, ya fada mani cewa a garin fatakwal ana saida lita a kan N180.”
“Saboda haka ina so in fada maku cewa za a samu man fetur, amma zai kasance da tsada a mafi yawan wuraren idan masu tasha suka cigaba da wannan.”
IPMAN ta ce abin da ya jawo wannan shi ne yankewar mai daga NNPC. Hakan ya sa aka bukaci a bar gidajen mai a bude dare da rana domin gudun fetur ya yi wahala.
Tallafin man fetur
Kwanakin baya ane aka ji shugaban Kamfanin Mai, NNPC, Mele Kyari ya na mai cewa farashin man fetur zai iya koma N320 zuwa N340 a tsakiyar wannnan shekarar.
Daga baya sai aka ji Gwamnatin tarayya ta dakatar da kokarin cire tallafin man fetur har sai yadda hali ya yi. Hakan ya na nufin za a cigaba da saida lita a kan N165.
Asali: Legit.ng