Dakarun Hisbah sun kama samari da yan mata 78 dake haɗa auren jinsi a Kano

Dakarun Hisbah sun kama samari da yan mata 78 dake haɗa auren jinsi a Kano

  • Hukumar Hisbah ta kama wasu mutane aƙalla 78 da take zargin suna haɗa auren jinsi tsakaninsu a cikin birnin Kano
  • Rahoto ya nuna cewa Dakarun Hisbah sun kai samame gidan da ake kira White House, suka kama mutanen da kuma kwaroron roba
  • A shekarar da ta shuɗe, hukumar ta taɓa kama wasu da take zargin suna haɗa auren jinsi, amma suka musanta zargin

Kano - Jami'an hukumar Hisbah sun samu nasarar kama wasu maza da mata akalla 78 da suke zargin suna shagalin haɗa auren jinsi a tsakanin su a jahar Kano.

Rahoton Aminiya ya nuna cewa yan sandan Musuluncin sun kame mutanen ne a Anguwar Nasarawa dake cikin ƙwaryar birnin Kano.

Hukumar Hisbah
Dakarun Hisbah sun kama samari da yan mata 78 dake haɗa auren jinsi a Kano Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Kazalika rahoto ya tabbatar da cewa an kama waɗan da ake zargin ne a wani gida mai suna White House, wanda ake zargin sanannen wuri ne na aikata biɗala a yankin.

Kara karanta wannan

Kotu ta sa a yi wa matashin ɗan kasuwa Bulala Bakwai a jihar Kaduna

BBC Hausa ta rahoto cewa dakarun Hisbah sun kama mutanen suna tsaka da tsagalin su a cikin gidan, kuma an gano kwaroron roba da yawa a tare da mutanen.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A halin yanzun mutum 78 Hisbah ta samu nasarar yin ram da su, wasu kuma da dama sun ranta ana kare, hukumar na cigaba da bin sawu da bincike kan lamarin.

Shin shagalin me mutanen ke yi a gidan?

A nasu ɓangaren, waɗan da ake zargi da haɗa auren jinsin, sun musanta tuhumar da ake musu, inda a cewarsu suna shagalin murnarn zagayowar ranar haihuwar abokin su ne (Birthday).

Legit.ng Hausa ta tattaro cewa ko a bara hukumar Hisbah ta kama wasu mutane da zargin auren jinsi a Kano, amma su ɗin ma daga baya suka musanta zargin.

A wani labarin na daban kuma Daga karshe, Tsohon gwamna ya bayyana jam'iyyar da ya koma bayan ficewa daga PDP

Kara karanta wannan

Kaduna: Kotun Shari'a Ta Tura Kishiyoyi 2 Zuwa Gidan Yari Saboda Faɗa Kan Mijinsu, Mijin Ya Ce Akwai Yiwuwar Ya Sake Su Duka

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Segun Oni, yace ya shiga jam'iyyar SDP kuma zai nemi takarar gwamna a zaɓen 18 ga watan Yuni.

Oni ya sanar da cewa jiga-jigan manyan jam'iyyun APC da PDP na goyon bayan takararsa ta gwamnan Ekiti.

Asali: Legit.ng

Online view pixel