Bayan watanni 9, kwamitin Amaechi ya kammala binciken wa'adin Hadiza Bala Usman a NPA

Bayan watanni 9, kwamitin Amaechi ya kammala binciken wa'adin Hadiza Bala Usman a NPA

  • Rotimi Amaechi ya kafa wani kwamiti da ya yi bincike a kan wa’adin Hadiza Bala Usman a NPA
  • Kwamitin Ministan bai samu Bala Usman da laifin satar Naira Biliyan 165 daga asusun hukumar ba
  • Binciken da aka yi ya nuna tsohuwar shugabar NPA ba ta ci kudi ba, amma ta rika sabawa Minista

Lagos - Rahoton The Cable ya bayyana cewa an wanke tsohuwar shugabar hukumar NPA ta kasa, Hadiza Bala Usman daga zargin satar kudi Naira Biliyan 165.

Zargin da ake yi wa Miss Hadiza Bala Usman na kin dawo da rarar biliyoyin da hukumar NPA ta samu cikin asusun gwamnatin tarayya, bai da madagora a doka.

Jaridar ta fitar da rahoto a ranar Talata, 15 ga watan Fubrairu 2022, ta ce kwamitin mutane 11 da Ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya kafa ya kammala aikinsa.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Naɗa Mohammed Bello Koko a Matsayin Shugaban NPA Mai Cikakken Iko

Wannan kwamiti bai samu Usman da laifin cin kudi ba, sai dai ana zargin ta da rashin da’a, ta na watsi da mai gidanta, ta na magana da shugaban kasa kai-tsaye.

Ya kamata a ce Hadiza Bala Usman ta na karbar umarni ne daga Rotimi Amaechi a lokacin da ta ke ofis, amma sai ta ke zuwa ga fadar shugaban kasa da kanta.

Hadiza Bala Usman
Rotimi Amaechi da Hadiza Bala Usman Hoto: politicos.ng
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haduwar Buhari da Amaechi

Rahoton ya bayyana cewa da Amaechi ya gabatar da takarda gaban shugaban kasa, ya na neman ya amince a sauke Bala Usman daga kujerarta, bai amince ba.

A lokacin Mai girma Muhammadu Buhari ya fadawa Ministan sufuri ya aikawa shugabar ta NPA takardar sammaci domin ta amsa laifin da ake zargin ta aikata.

Majiya ta shaidawa manema labarai cewa Usman ta kare kanta a gaban kwamitin da aka kafa. Shugaban kasa ya nemi a ba tsohuwar MD damar wanke kanta.

Kara karanta wannan

Buhari ya mika wa majalisa karin kasafin kudi, ciki har da na tallafin man fetur N2.557tr

A karshe dai Ministan kasar ya zagaya, ya bukaci Sakataren din-din-din na ma’aikatar sufuri na tarayya, Magdalene Ajani ta rubuta takarda zuwa ga Bala Usman.

A martanin da ta bada a Junairun 2022, Bala-Usman ta karyata zargi 10 da aka yi mata. Daga ciki har da sayen kaya ba tare da izini ba da kuma saba umarnin kotu.

Tun a watan Mayun 2021 aka kafa wannan kwamiti, amma sai yanzu ne ake jin labarin binciken.

Koko zai rike NPA

Dazu aka ji Shugaba Buhari ya amince da nadin Mohammed Bello Koko a matsayin shugaban hukumar tashoshin jiragen ruwa ta Najeriya, NPA na din-din-din.

Mohammed Bello Koko wanda ya yi aiki da gwamnatin jihar Ribas a lokacin Rotimi Amaechi ya canji Bala Usman wanda aka sauke daga wannan mukami a 2021.

Asali: Legit.ng

Online view pixel