Innalillahi: 'Yan bindiga sun sake addabar yankunan Katsina, an sake kulle makarantu, hakimai sun yi kaura

Innalillahi: 'Yan bindiga sun sake addabar yankunan Katsina, an sake kulle makarantu, hakimai sun yi kaura

  • Farfesa San Lugga, Wazirin Katsina, ya koka kan hare-haren da yan bindiga ke ci gaba da kaiwa yankunan jihar Katsina
  • Lugga ya ce a yanzu haka an sake rufe makarantu sannan hakimai sun yi kaura zuwa garin Katsina a kananan hukumomi takwas saboda hare-haren ta'addancin
  • Ya ce babu ranar duniya da ba za a kashe rai ko sace wani ba a Katsina tun kimanin shekaru biyu da rabi da suka shige

Katsina - Wazirin Katsina, Farfesa San Lugga ya bayyana cewa yawan hare-haren yan bindiga ya yi sanadiyar rufe makarantu a kananan hukumomi takwas na jihar Katsina.

Farfesa Lugga ya bayyana cewa hakiman kananan hukumomin takwas sun koma Katsina, babbar birnin jihar da zama sakamakon hare-haren.

Wazirin Katsinan ya bayyana hakan ne a garin Ilorin, jihar Kwara a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, a wajen wani taro da cibiyar zaman lafiya ta IPCR ta shirya, jaridar The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gwamnatin Katsina ta haramta kungiyar Yan-Sa-Kai a fadin jihar

Innalillahi: 'Yan bindiga sun sake addabar yankunan Katsina, an sake kulle makarantu, hakimai sun kama gabansu
'Yan bindiga na ci gaba da addabar yankunan Katsina Hoto: Channels TV
Asali: UGC

Farfesa Lugga ya kuma ce an kulle manyan hanyoyin jihar guda biyu don zirga-zirgar ababen hawa saboda ayyukan ‘yan bindiga.

Ya ce ya yi aiki a kwamitocin shugaban kasa kan tsaro guda 48 a kasar, amma ya koka kan cewa shawarwarin kwamiti daya kadai aka aiwatar.

Ya kuma yi bayanin cewa tun shekaru biyu da rabi da suka gabata, babu ranar da ba za a kashe rai ko yin garkuwa da wani ba a jihar Katsina, inda ya bayyana lamarin a matsayin yaki ba rikici ba, rahoton Vanguard.

Ya ce:

“A karon farko, a iya sanina, shugaban kasa Goodluck Jonathan ne ya aiwatar da shawarar da kwamitin shugaban kasa kan tsaro. Wannan ne dalilin da yasa aka yi zabuka cikin lumana a jihar Borno a 2015 ba tare da an zubar da jini ba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shafe tsawon kwanai 3 suna kai mamaya garuruwan wata jiha a arewa

“Mambobin kwamitin sun yi aiki ba dare ba rana, inda suka zanta da manyan kwamandojin Boko Haram banda Shekau wanda ya ki shiga tsarin. Bayan tattaunawa cikin nasara, sai suka amince suka janye wuta.”

Rashin tsaro: Gwamnatin Katsina ta haramta kungiyar Yan-Sa-Kai a fadin jihar

A gefe guda, gwamnatin jihar Katsina a ranar Litinin, 14 ga watan Fabrairu, ta sanar da haramta kungiyar Yan-sa-kai a jihar, jaridar Punch ta rahoto.

Gwamnatin ta bayyana cewa ta dauki matakin ne saboda yawan laifukan da mambobin kungiyar ke aikatawa.

Kungiyar na dauke ne da mutanen da suka sadaukar da kansu domin taimakawa a lamuran tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel