'Yan Najeriya sun caccaki hadimin Buhari saboda rubutun da ya wallafa a Twitter

'Yan Najeriya sun caccaki hadimin Buhari saboda rubutun da ya wallafa a Twitter

  • Wasu yan Najeriya ma'abota amfani da shafin dandalin sada zumunta na Twitter sun caccaki, Bashir Ahmad, hadimin Shugaba Muhammadu Buhari
  • Hakan ya biyo bayan wani rubutu ne da ya wallafa da ke cewa 'idan har abu ya fi karfin mutum toh kada ya yarda abin ya jefa shi cikin damuwa'
  • Wasu dama sun yi wa rubutun fassarar cewa gwamnatin Buhari ta bari Najeriya ta cigaba da zama cikin matsaloli ne saboda abin ya fi karfinsu

Wasu masu amfani da shafin sada zumunta na Twitter sun yi martani kan wani rubutu na karfafa gwiwa da Bashir Ahmed, hadimin Shugaba Muhammadu Buhari a bangaren sabbin kafafen sada zumunta ya wallafa.

Ya rubuta cewa:

"Abu mai muhimmanci!!! Idan lamari ya fi karfin ka toh kada ka bari ya dame ka."

Kara karanta wannan

Mun shiga uku: Tsadar man fetur ya sa 'yan Najeriya kuka, sunyi zazzafan martani

Yan Najeriya sun caccaki hadimin Buhari saboda rubutun da ya wallafa a Twitter
Rubutun da hadimin Buhari ya wallafa a Twitter ya janyo maa caccaka. Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A martanin da suka yi, wasu yan Najeriya a Twitter sun alakanta rubutun da gwamnatin mai gidan Bashir, wato Shugaba Muhammadu Buhari.

Ga wasu daga cikin abubuwan da yan Najeriyan suka ce:

Omosalewa ta ce:

"Yanzu mun san dalilin da yasa Najeriya ta tsinci kanta a halin da ta ke karkashin mulkin jam'iyyar APC da Muhammadu Buhari. Halin da ke kasar ya fi karfinsu kuma ba za su bari ya dame su ba, ba abin da ya dame su."

Osas @freedommat19 ya ce:

"Dama wannan shine dalilin da yasa Najeriya ke nutsewa? Abin ya fi karfin masu gidanka sai suka yi watsi da shi don kada ya jefa su cikin damuwa. Sai suka kyalle kasar ta sake nutsewa."

Onuoha Okechukwu #link2ok08 ya ce:

"Ko da yaushe, komai ya fi karfin ku a Aso Rock. Toh, mun gane. Yan Najeriya ku yi hakuri, abin ya kusa wucewa."

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun sace matar mataimakin shugaban PDP, da wasu mutum 10 a Abuja

Amma akwai wasu wadanda suka yi wa rubutun fahimta kamar yadda ya ke a zahiri

Oluwafemi Popoola ya wallafa:

"Na gode. Wannan shine abin da na ke bukata a yanzu."

#SimplestJabir, ya ce:

"Akwai wani abin da ke damu na amma na san komai na hannun Ubangiji."

Asali: Legit.ng

Online view pixel