Sheikh Gadon Kaya: An yi min gurguwar fahimta game da batun mata ma'aikatan kiwon lafiya

Sheikh Gadon Kaya: An yi min gurguwar fahimta game da batun mata ma'aikatan kiwon lafiya

  • Dr. Abdallah Usman Gadon Kaya ya magantu a kan cece-kuce da ake yi game da wasu kalamai da ya yi kan ma'aikatan asibiti
  • Shehin malamin ya janye kalaman nasa inda ya ce an yi masa gurguwar fahimta ne
  • Tun farko dai an jiyo malamin yana fadi a wani bidiyonsa da ke yawo cewa mata da ke aikin dare su kan yi fasikanci a dakunan asibiti

Shahararren malamin nan na addinin Musulunci, Sheikh Abdallah Usman Godon Kaya, ya janye kalamansa a kan matan asibiti na cewa wasunsu na aikata alfasha a yayin da suke bakin aikin dare.

Tun farko dai Shehin malamin wanda ya shahara wajen yin wa’azi, ya zargi ma’aikatan jinya da mu’amalar banza da suka hada da lalata da cin zarafin mata a cikin wani bidiyo.

Kara karanta wannan

Zargin matan asibiti da fasikanci: Budaddiyar wasika zuwa ga Dr. Abdallah Gadon-Kaya

Sai dai kuma, a yanzu malamin ya janye kalamansa bayan da kungiyar ma’aikatan jinyan ta nemi ya janye furucinsa domin a cewarta hakan bata wa mambobinta suna ne, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.

Sheikh Gadon Kaya: An yi min gurguwar fahimta game da batun mata ma'aikatan kiwon lafiya
Sheikh Gadon Kaya: An yi min gurguwar fahimta game da batun mata ma'aikatan kiwon lafiya Hoto: Martaba FM
Asali: UGC

Sheikh Gadon-kaya ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ban yi niyyar cutar da kowa ba, kuma ya kamata mutane su zama masu kyautata tunanin alheri."

A hirarsa da BBC, shehin malamin ya kuma ce wasu ma'aikatan lafiya ne suka fara tuntubarsa kan wannan lamarin da ke ci gaba da janyo cece-kuce a tsakanin mutane.

Ya ce:

"Wasu ma'aikatan kiwon lafiya biyu, namiji da mace ne suka kira ni, muna karatu ne suka yi min fatawa, inda suka fadi matsalar da suke fuskanta ta hada mace da namiji, wani lokacin a cikin aiki na dare.
"Suka koka, kuma na yi bayani a matsayina na almajiri, mai nusantar da mutane akan aikata daidai."

Kara karanta wannan

Duk a cikin so ne: Saurayi ya kaftawa budurwarsa mari sannan ya roki ta aureshi

Ya ce ya yi bayani ne cewa matukar hakan na faruwa ya kamata a gyara domin tsare mutunci matan gaba daya.

Ya kuma bayyana cewa ya zauna da ma'aikatan jinyan bayan da kalamansa suka tayar da hankalin mutane inda suka tattauna.

Ya ce:

"Mun zauna da su, sun warware min dukkan abubuwan da suka shige min duhu kan wannan lamarin."

Har ila yau, ya ce sun sanar da shi cewa labarin da ya yada babu gaskiya a cikinsa, inda shi kuma ya ce ya dogara ne da kiran da wasu ma'aikatansu suka yi masa.

"Wasu ma'aikatanku ne suka kira ni, suka tambaye ni a karatu kuma na bayar da jawabi, inda na ce a gyara.
"Laifina shi ne na ce idan wannan abin yana faruwa, na ce a gyara."

Sannan a cewarsa, dalilinsa na biyu na furta wadannan kalaman da suka haddasa kace-nace shi ne saboda yana cikin masu yin kira ga al'umma da a rungumi karatun kiwon lafiya domin saboda akwai bukatar su cikin al'ummar kasar.

Kara karanta wannan

Annabin 'yan Twitter: Wani ya yi da'awar shi Annabin Allah ne, ya shiga hannun hukuma

A karshe malamin ya ce bayanan da ma'aikatan lafiya suka yi kan batun, ya karu da wasu abubuwan da a baya bai sani ba.

Sai dai ya kare kansa inda ya ce bai ambaci sunan inda matar da ta yi masa tambayar ta fito ba.

"Ban san daga wace jiha tambayar ta fito ba kuma ban ambaci sunan wata jiha ba, ballantana wasu suce da su nake wannan maganar."

Zargin matan asibiti da fasikanci: Budaddiyar wasika zuwa ga Dr. Abdallah Gadon-Kaya

A gefe daya, Legit.ng Hausa ta samu wasikar da Malam Ibrahim El-Caleel ya rubutawa Abdallah Usman Gadon Ƙaya da ya jefi ma’aikatan jinya da mummunar alfasha.

A wannan budaddiyar takarda da Ibrahim El-Caleel ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ja hankalin babban malamin addini, Abdallah Gadon Ƙaya.

El-Caleel ya yi masa nasiha da ya kiyaye abin da yake fada a matsayinsa na wanda ake sauraron maganarsa, tare da jan-kunnensa kan daukar jita-jita.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Likitan Bello Turji da ke masa jinya da kawo masa kwaya ya shiga hannu

Asali: Legit.ng

Online view pixel