2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Tsohon mataimakin gwamnan CBN

2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Tsohon mataimakin gwamnan CBN

  • Tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Kingsley Moghalu, ya magantu a kan aniyarsa ta tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Moghalu ya ce ya manta bai sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari muradinsa na son gadar kujerarsa a babban zaben 2023 mai zuwa ba
  • Furucin dan siyasar na zuwa ne bayan manyan yayan APC, Bola Tinubu da Dave Umahi sun ce sun sanar da Buhari aniyarsu na neman kujerar shugaban kasa a zabe mai zuwa

Mai burin zama shugaban kasa, Kingsley Moghalu, ya bayyana cewa ya manta bai sanar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari aniyarsa na takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba.

Daily Post da Punch sun rahoto cewa, Moghalu wanda ya kasance tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, 12 ga watan Janairu, a shafinsa na Twitter.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Moghalu
2023: Na manta ban sanar da Buhari zan yi takarar shugaban kasa ba - Moghalu Hoto: Daily Post
Asali: UGC

Ya wallafa a shafin nasa:

“Na manta ban sanar da Shugaban kasa @Mbuhari cewa zan yi takarar shugaban kasa ba. Amma na sanar da yan Najeriya, wanda shima yana daya daga cikinsu, don haka babu matsala.”

Dan siyasar ya kuma kasance dan takarar Shugaban kasa na jam’iyyar Young Progressive Party (YPP) a 2019 amma ya sha kaye a hannun Buhari.

Ya koma jam’iyyar African Democratic Congress a 2021 sannan ya kaddamar da aniyarsa na takarar kujerar a 2023.

Wallafar da Moghalu yayi ya biyo bayan ayyana batun tsayawa takara da babban jigon APC na kasa, Bola Tinubu da Gwamnan jihar Ebonyi, Dave Umahi suka yi na cewa za su tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Manyan mambobin na APC sun ziyarci Buhari a lokuta daban-daban a fadar shugaban kasa don sanar masa da aniyarsu na takara a zaben shugaban kasa mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Shahararren tsohon gwamnan APC na shirin shiga tseren neman kujerar Buhari

Shugaban kasa a 2023: Na shirya yin gaba da gaba da Tinubu a zaben fidda gwanin APC – Shahararren sanata

A wani labari na daban, bulaliyar majalisar dattawa, Orji Uzor Kalu, ya ce a shirye yake ya yi takarar tikitin shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tare da jigon jam'iyyar na kasa, Bola Tinubu, idan aka mika shi yankin kudu.

Kalu ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a ranar Litinin, 10 ga watan Janairu.

Tsohon gwamnan na jihar Abia ya ce ya yarda cewa zagayen kudu maso gabas ne samar da shugaban kasa na gaba, rahoton The Cable.

Asali: Legit.ng

Online view pixel