NSCDC ta cafke wata mata mai shekaru 35 kan satar akuya 22 a Bauchi

NSCDC ta cafke wata mata mai shekaru 35 kan satar akuya 22 a Bauchi

  • Hukumar NSCDC ta kama wata Zainab Malam Barka mai shekaru 35 ‘yar karamar hukumar Katagum a jihar Bauchi bisa zarginta da satar akuyoyin jama’a
  • Yayin tasa keyarta, kakakin hukumar, SC Garkuwa Y. Adamu ya bayyana yadda Zainab ta ke satar da taimakon wani Usman Abubakar mai shekaru 50
  • Kakakin ya bayyana yadda ta sace akuyoyi 22 a lokuta daban-daban sannan ta sayar da 8 din farko a kasuwar Hardawa a N77,000

Bauchi - Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Bauchi ta kama wata Zainab Malam Barka mai shekaru 35 daga anguwar Madara da ke karkashin karamar hukumar Katagum bisa zarginta da satar awaki, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Yayin tasa keyar wacce ake zargi, kakakin hukumar, SC Garkuwa Y. Adamu ya bayyana yadda Zainab ta ke satar da taimakon wani Usman Abubakar mai shekaru 50 wanda ya kware a satar awaki.

Kara karanta wannan

Aisha Buhari za ta karba bakuncin taron farko na PWC a Abuja

NSCDC ta cafke wata mata mai shekaru 35 kan satar akuya 22 a Bauchi
Matar da ta saci akuya 22 a Bauchi ya shiga hannu. Hoto: Nigerian Tribune
Asali: Facebook

A cewar kakakin, bincike ya nuna yadda ta sace awaki 22 yayin da ta je satar sau biyu, da farko ta fara satar awaki 8 ne a ranar 23 ga watan Disamban 2021 inda ta wuce da su kasuwar Hardawa ta sayar da su N77,000.

Nigerian Tribune ta bayyana yadda Garkuwa Adamu ya shaida yadda bayan mako daya ta sake komawa anguwar da ta yi satar da farko ta sace guda 14 wadanda ta zarce da su kasuwar Misau.

Asirinta ya tonu ne bayan jami’an NSCDC sun kama ta da awaki 14

Sai dai kadarinta ya cika bayan jami’an NSCDC da ke aiki a Misau su ka yi ram da ita sannan su ka gurfanar da ita a kotu bayan kammala bincike.

Kara karanta wannan

Mai tsaron shago ya yi ɓadda-kama, ya yi barazanar sace mai gidansa, ya nemi a bashi N1.5m

Kakakin ya kara da bayyana yadda a karkashin shugabancin kwamanda Nuraddeen Abdullahi aka samu nasarar kama wasu ‘yan bangar siyasa wadanda aka fi sani da Sara-suka sakamakon ta’addanci.

A cewarsa, wadanda aka kama suna da hannu a addabar garin Misau, hedkwatar, karamar hukumar Misau da ke jihar.

Ya kara da bayyana yadda a ranar 5 ga watan Janairun 2022 da misalin karfe 11 na dare aka kira su daga cikin garin Misau akan ‘yan Sara-suka sun addabi jami’a.

Take a nan aka kama ‘yan Sara-suka 2

Hakan ya sa shugaban ofishin yankin Misau ya tura yaransa wadanda su ka kama mutane 2 daga cikin ‘yan daban.

Cikin wadanda aka kama akwai wani Auwal Usman mai shekaru 17 da Ibrahim Ibrahim mai shekaru 18, duk ‘yan garin Misau.

Kakakin yace bincike ya nuna yadda suke amfani da wuka wurin kai wa mutane farmaki don yanzu haka akwai mutane 4 da suka yanka wadanda ke FMC Azare ana kulawa da lafiyarsu.

Kara karanta wannan

Jami’ar Kano Ta Ɗage Yin Jarrabawa Saboda Yajin Aikin Masu Baburan A-Daidaita-Sahu

Binciken ya kara bayyana yadda suka kware wurin kwacen kaya daga hannun mutane kuma ana ci gaba da binciko sauran abokan ta’addancinsu.

Rundunar ta tabbatar da cewa jami’anta za ta jajirce wurin ganin ta samar da tsaro ga jama’an gari matsawar sun bayar da hadun kai sannan sun dinga kai rahoto da zarar sun samu wani bayani a kan ‘yan ta’adda.

Bauchi: Gobara ta lakume babban kasuwar kayan abinci, an yi asarar kayan miliyoyin naira

A wani labarin, mummunar gobara ta afka shaguna cike da kayan abinci makil masu kimar miliyoyi a wani bangare na sananniyar kasuwar kayan abinci ta Muda Lawal da ke jihar, Vanguard ta ruwaito.

An gano yadda wutar ta fara ruruwa da tsakar daren Laraba wacce ta ci gaba da ci har safiyar Alhamis inda ta janyo mummunar asarar kafin jama’a da taimakon ‘yan kwana-kwana su kashe wutar.

Duk da dai ba a gano sababin wutar ba, amma ganau sun ce daga wani shago wanda danyun kayan abinci su ke cikinshi ta fara bayan an kawo wutar lantarki.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi garkuwa da tsohon kakakin majalisa, Duruji

Asali: Legit.ng

Online view pixel