Mai tsaron shago ya yi ɓadda-kama, ya yi barazanar sace mai gidansa, ya nemi a bashi N1.5m

Mai tsaron shago ya yi ɓadda-kama, ya yi barazanar sace mai gidansa, ya nemi a bashi N1.5m

  • Hukumar NSDC reshen jihar Ekiti ta kama wani mai tsaron shago, Tobilona Olayinka, bisa zargin kulle-kullen garkuwa da mai shagon da yake tsaro don tatsar naira miliyan 1.5
  • Kwamandan NSCDC na jihar, Mr John Fayemi ya ce wanda ake zargin ya rubuta wa mutumin wasika ne a watan Disamba yana ikirarin matsawar ba a tura masa N1.5m ta banki ba zai sace shi
  • Fayemi ya bayyana hakan ne yayin da ya tasa keyar wanda ake zargin tare da wasu mutane biyu a cikin sabuwar shekarar nan inda ya ce jami’an hukumarsu ne su ka yi ram da su saboda ta’addanci

Ekiti - Jami’an hukumar NSCDC na jihar sun samu nasarar kama wani mai tsaron shago, Tobiloba Olayinka, bisa zarginsa da shirya kulle-kullen garkuwa da mai shagon da yake tsaro duk don tatsar N1.5m daga wurinsa, The Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugabanci a 2023: Kwankwanso ya bayyana dalilin da yasa ba za a ba 'yan kudu dama ba

Kwamandan NSCDC na jihar, Mr John Fayemi ya ce wanda ake zargin ya rubuta wasika ne da sunan bogi yana ikirarin yin garkuwa da mai shagon da yake tsaro matsawar bai tura masa naira miliyan 1.5 a asusun bankinsa ba.

Mai tsaron shago ya yi ɓata kama, ya yi barazanar sace mai gidansa, ya nemi a bashi N1.5m
Yaro mai tsaron shago ya yi barazanar sace mai gidansa, ya nemi a bashi N1.5m. Hoto: The Nation
Asali: UGC

Fayemi ya bayyana yadda lamarin ya auku yayin tasa keyarsa tare da wasu matasa biyu inda ya ce sun aikata laifuka daban-daban a sabuwar shekarar nan.

The Punch ta labarta yadda matashin mai shekaru 21 ya yi yunkurin garkuwa da wanda ya ke yi wa aiki yayin amma bai ci nasara ba, don jami’an sun yi ram da shi.

Bincike ya fallasa matashin

A cewarsa:

“Bayan bincike mai tsawo, an kama matashin a ranar 8 ga watan Janairun 2022. Dama ya na tsare wa mutumin shago ne, amma sai ya shirya wata wasika da suna na daban da lambar asusun banki ya na bukatar naira miliyan 1.5 ko kuma ya sace wanda ya ke yi wa aikin.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: 'Yan sanda sun shiga tsakani yayin da kwarto ya kashe mijin daduronsa

“Sai dai sakamakon kokarin yara na, an yi gaggawar nemo shi. Ya yi amfani da wani suna, lambar asusun banki da kuma wata lambar waya na daban don ya yi damfara. Daga nan mu ka binciko lambar wayar sannan mu ka kama shi. Za a gurfanar da shi a kotu da zarar an kammala bincike.”

Olayinka ya ce ya so yin amfani da kudin don shan jarmiya a kirsimeti ne

Olayinka, wanda asali dan jihar Osun ne ya ce ya yi kokarin tatsar kudi ne daga hannun wanda ya ke yi wa aikin don cin bikin kirsimeti.

Kamar yadda ya ce:

“Ban so yin garkuwa da shi ba. Na zaci da na yi barazanar zai turo kudin. Na so yin amfani da kudin ne don shagalin kirsimeti, hakan yasa na tura masa wasikar da kuma lambar asusun bankin kuma bai kai ga tura min naira miliyan 1.5 din ba aka kama ni.”

Har ila yau, an kama wani Ayodeji Fanas mai shekaru 21 bisa zarginsa da satar N500,000 bayan yin basaja da sunan zai taimaka wa wani wurin sayar masa da abin hawa da kuma wani Daniel Emmanuel wanda ake zargin ya sace wasu karafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel