Hotunan Buhari ya na tattakin mita 800, Obasanjo ya na kwallo, Jonathan ya na sassarfa
1 - tsawon mintuna
- Atisaye ya na da matukar amfani wurin tabbatar da lafiyar jiki da na kwakwalwa, kamar yadda masana kimiyya ke bayyanawa
- Shugabannin kasashen duniya suna yin wasanni daban-daban domin motsa jiki duk da tarin ayyukan da ke gabansu
- An ga hoton shugaba Buhari ya na tattakin mita dari takwas, Jonathan ya na sassarfa yayin da Obasanjo ke wasan kwallon kafa
Atisaye a yanzu ba wai jijjiga bane har a yi zufa ba. Masana kimiyya sun gano alaka tsakanin lafiyar jiki a bayyane da kuma karfin kwakwalwa. Ana mamakin dalilin da yasa shugabannin duniya ke atisaye duk da yawan ayyukan da ke kansu.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya na yin wasan kwallon doki. Firayim ministan Canada, Justin Trudeau, ya kan yi wasan dambe.
Hakazalika, ba a bar shugabannin Najeriya a baya ba, shugaban kasa Muhammadu Buhari na yin tattaki, tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya na wasan kwallon kafa yayin da Jonathan na yin sassarfa.
Ga hotunan shugabannin Najeriyan yayin da suke tsinka jini.
Asali: Legit.ng