Matsalar tsaro: CAN ta maida martani ga gwamna Masari kan kalaman mallakar makamai

Matsalar tsaro: CAN ta maida martani ga gwamna Masari kan kalaman mallakar makamai

  • Kungiyar CAN ta bayyana abin da take gudu matukar mutane suka ɗauki shawarar gwamnan Katsina, Aminu Masari
  • CAN tace idan mutane suka mallaki makamai to jami'an tsaro za su koma kama su maimakon yan ta'adda
  • A karo na biyu, Masari ya sake nanata shawaran sa cewa mutane su ta shi tsaye su nemi makamin kare kan su daga harin yan bindiga

Katsina - Kungiyar kiristoci a Najeriya (CAN) tace kalaman gwamna Masari na jihar Katsina na mutane su mallaki makamai ba sabon abu bane.

CAN ta bayyana cewa abin da take gudu shi ne hukumomin tsaro su yi amfani da wannan damar su rinka kame mutanen da ba ruwansu waɗan da suka ɗauki shawarar gwamnan.

Mataimakin shugaban CAN (yankin arewa), Rabaran John Hayab, shine ya faɗi haka a wata hira da Vanguard ranar Laraba a Abuja.

Kara karanta wannan

Innalillahi: 'Yan bindiga sun kutsa gidaje a Zamfara, sun hallaka wani basarake

Gwamnan Katsina, Aminu Masari
Matsalar tsaro: CAN ta maida martani ga gwamna Masari kan kalaman mallakar makamai Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Ya kuma ƙara da cewa kalaman Masari sun nuna ƙarara cewa hukumomin tsaro ba su da karfin iya shawo kan ayyukan yan ta'adda.

Hayab yace:

"Kalaman gwamna Masari na kare kai ba sabon abu ba ne. Abin damuwar shi ne, hukumomin tsaron mu za su yi amfani da wannan damar su kame mutane, waɗan da laifin su shine sun mallaki makaman kare kai."
"Yayin da kuma waɗan da ke aikata ta'addancin ba za'a kama su ba. Idan gwamna mai ci zai cigaba da maimaita irin wannan kalaman, domin karo na biyu kenan, to ina gani yasan cewa jami'an tsaro ba za su iya nasara kan yan bindiga ba."

Akwai babbar matsala - CAN

Hayab ya kara da cewa abun takaici ne shugabanni, waɗan da mutane ke fatan su kawo karshen lamarin, amma su koma suna ba su wannan shawaran.

Kara karanta wannan

Zamu taimaki mutane su mallaki bindigu domin kare kansu daga sharrin yan bindiga, Gwamna

"Akwai damuwa idan har shugabanni zasu shawarci mutane, waɗan da ke jiran wani ikon Allah ya sa a kawo karshen yan bindiga, su ne za su ta shi su yi aikin da kan su."
"Waɗan da mu ke addu'a da fatan za su kawo mana karshen wannan matalar, su ke cewa ba za su iya taimakon mu ba."

A wani labarin kuma CAS ya umarci dakarun sojoji su cigaba da ruwan wuta har sai sun aika baki daya yan bindiga lahira

Shugaban rundunar sojin sama a Najeriya (NAF) ya umarci sojojinsa su cigaba da aikin kai hare-hare kan yan bindiga har sai sun karar da su baki ɗaya.

CAS ya bukaci sojojin kada ku dakata da ruwan wutan da suke wa yan ta'adda a sassan ƙasar nan, domin sun zama barazana ga cigaban Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel