Rashin tsaro: Yadda ‘Yan bindiga suka yi awon-gaba da wani Basarake a Arewacin Najeriya

Rashin tsaro: Yadda ‘Yan bindiga suka yi awon-gaba da wani Basarake a Arewacin Najeriya

  • Miyagun ‘Yan bindiga sun je har gidan Sarkin kasar Gindiri, sun yi awon gaba da shi cikin tsakar dare
  • Wani ‘danuwan Basaraken, Charles Mato Dakat ya bada labarin yadda aka zo har gida aka yi gaba da shi
  • Sai da ‘yan bindigan suka dauki awa guda su na kokarin dauke Sarkin ba tare da an iya kawo dauki ba

Plateau - Daya daga cikin ‘yanuwan Sarkin kasar Gindiri, karamar hukumar Mangu, jihar Filato, Charles Mato Dakat, ya bada labarin yadda aka dauke shi.

Daily Trust ta rahoto Charles Mato Dakat ya na cewa an dauke Sarkin ne a safiyar Lahadi, 26 ga watan Disamba, 2021, har yanzu ba a san inda ya shiga ba.

A cewar Charles Dakat, ‘yan bindiga sun shiga gidan mai martaban ne wajen karfe 1:30 na dare, amma suka gagara shiga gidan cikin sauki saboda an rufe.

‘Dan uwan Basaraken yake cewa ‘yan bindigan sun shafe kusan sa’a guda kafin su bar gidan Sarkin Mangu, a karshe suka yi nasarar yin awon gaba da shi.

“Bayan shiga gidan ta kofa ya yi masu wahala, sai suka rusa bangaren katangar, sannan suka karya tagar gidan, kafin su iya yin awon gaba da basaraken.”
“Sun zo gidan da kimanin karfe 1:30 na dare, su ka tafi da karfe da 2:30 na dare.”

- Charles Mato Dakat

Simon Lalong
Gwamnan Filato, Simon Lalong Hoto: @LalongBako
Asali: Twitter

Rahoton na Daily Trust ya bayyana cewa har zuwa safiyar Laraba, 29 ga watan Disamba, 2021, babu wani labari game da inda ‘yan bindigan suka kai Sarkin.

Mai magana da yawun bakin dakarun, Operation Safe Heaven, Manjo Ishaku Takwa, yace jami’ai sun bazama yankin domin a ceto Sarkin daga hannun miyagu.

An kafa Operation Safe Heaven (OPSH) ne domin kawo zaman lafiya a yankin yayin da ‘yan bindiga suke cigaba da yi wa Bayin Allah ta’adi dare da rana.

Mai magana da yawun bakin rundunar ‘yan sanda na jihar Filato, ASP Ubah Gabriel, ya tabbatar da cewa dakaru su na kan aiki domin a tona asirin ‘yan bindigan.

Rashin tsaro a Katsina

An ji cewa Gwamnan Katsina, Aminu Bello Masari ya bada shawara ga mutanensa su nemi makamai, yace duk wanda ya mutu wajen kare kansa, ya yi shahada.

Rt. Hon. Masari yace ba zai yiwu jama’a su zauna haka kurum ana kawo masu hari ba su da bindiga ba, don haka ya bada shawarar kowa ya tanadi makaminsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel