An rasa rayuka, an sace wasu yayin da ‘Yan bindiga suka yi ta’adi a titin Zaria zuwa Kaduna
- Miyagun ‘Yan bindiga sun yi barna a titin Kaduna zuwa garin Zaria a yammacin ranar Litinin dinnan
- Ana zargin mutane da-dama sun mutu a wannan hari da aka kai, sannan an yi garkuwa da Bayin Allah
- Wata majiya tace sojoji sun yi kokari wajen kubuto wasu daga cikin wadanda aka nemi ayi gaba da su
Kaduna - Matafiya da-dama sun gamu da tashin hankali a sa’ilin da ‘yan bindiga su ka tare titin Kaduna-Zaria a cikin daren ranar Litinin, 13 ga watan Disamba.
Legit.ng Hausa ta samu labari an kashe mutane, sannan kuma an yi garkuwa da wasu a sakamakon mummunan harin da ‘yan bindiga suka kai a jiya.
Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta tabbatar da rahoton dazu da safe, ‘yan bindigan sun yi ta’adi a daidai unguwar Kofar Gayan da ke bakin shigowa garin Zaria.
Miyagun ‘yan bindigan sun tare masu bin hanyar na Kaduna zuwa Zaria ne da kimanin karfe 8:00 na dare, da nufin su yi garkuwa da Bayin Allah, su karbi fansa.
Sojoji sun ceto wasu matafiyan
Wasu wadanda abin ya faru a gaban idanunsu, sun ce miyagun sun kama fasinjoji da dama, suka shiga cikin jeji da su, kafin zuwan jami’an sojoji da suka ceto wasu.

Asali: UGC
Wani daga cikin fasinjoji ya shaidawa Daily Nigerian cewa an dauki mutane, kuma an harbe wasu. Sojoji sun ceto wasu daga cikin wadanda aka dauke.
A halin yanzu ana fama da matsalar rashin tsaro tsakanin wannan yanki har zuwa garin Jaji a jihar Kaduna, inda ake da dakarun sojojin kasa rututu a jibge.
Mutum daya ya mutu a harin
Wata majiya tace mutanen da aka dauke a hanyar za su haura 30, ta kuma ce an hallaka mutum daya.
Da yake bayani a Facebook, wani Bawan Allah mai suna Nura Lawal Abubakar, ya tabbatar da mutuwar Alhaji Sani Dogara a wannan hari da aka kai a jiya.
Heenatuh Bint Rasheed tace ta na cikin wadanda suka sha da kyar daga hannun ‘yan bindigan.
“Kaduna - Zaria high way mun Sha.... Inna lillahi wa Inna ilaihi rajiun.... Allah ka kubutar da Wanda aka kwashe....”
“ArewaIsBleeding, #MyArewa, #SecureNorth.”
- Heenatuh Bint Rasheed
Zuwa yanzu babu labarin adadin wadanda aka sace, hallaka ko aka ji wa rauni a harin. Jami’an ‘yan sanda na reshen jihar Kaduna ba su yi magana ba tukuna.
Asali: Legit.ng