Wata sabuwa: Gwamnan Zamfara ya tafi neman taimakon shugaban Nijar kan batun 'yan bindiga

Wata sabuwa: Gwamnan Zamfara ya tafi neman taimakon shugaban Nijar kan batun 'yan bindiga

  • Gwamnan jihar Zamfara ya dura a jamhuriyar Nijar domin tattauna batutuwan da suka shafi matsalar tsaro
  • Gwamnan ya bayyana cewa, zai tallafawa gwamnatin jamhuriyar Nijar domin magance matsalolin tsaro a yankin Arewa maso yamma
  • Shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya bayyana goyon bayansa ga gwamnan ya kuma gode masa da ziyara

Zamfara - Gwamna Bello Mohammed Matawalle na jihar Zamfara, a ranar Litinin, ya gana da shugaban jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum, a wani bangare na kokarin kawo karshen duk wani nau'in 'yan bindiga a Najeriya da Jamhuriyar Nijar.

Sakataren yada labarai na gwamnan, Jamilu Iliyasu Birnin Magaji, ya ce shugabannin biyu sun gana ne a fadar shugaban kasa dake Yamai, Daily Trust ta ruwaaito.

Matawalle, gwamnan jihar Zamfara
Wata sabuwa: Gwamnan Zamfara ya tafi neman taimakon shugaban Nijar kan matsalar 'yan bindiga | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Gwamna Bello Matawalle ya samu rakiyar Sanata Sahabi Yau Kaura mai wakiltar mazabar Zamfara ta Arewa da dan majalisar tarayya mai wakiltar mazabar Gummi/Bukkuyum a majalisar wakilai ta tarayya, Injiniya Suleiman Abubakar Mahmoud Gummi.

Kara karanta wannan

Rikicin APC a Zamfara: Tsohon kwamishina ya bar tsagin Yari ya koma na Matawalle

Hakazalika da babban sakataren gwamna Lawal Umar Maradun da dai sauransu manyan kusoshin gidan gwamnati, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Taron dai an yi shi ne domin tattauna batutuwan da suka shafi tabarbarewar tsaro musamman a yankin Arewa maso yammacin Najeriya da jamhuriyar Nijar tare da kudurta aniyar binciko wasu fannonin tallafi da hadin gwiwa tsakanin Jamhuriyar Nijar da jihar Zamfara.

Gwamna Matawalle ya yi wa shugaba Bazoum bayanin irin matakan da gwamnatinsa ke dauka na kawo karshen duk wani nau'i na miyagun laifuka a yankin.

Gwamnan ya ce baya ga shirin zaman lafiya da sulhun da ya kaddamar, gwamnatinsa ta baiwa jami’an tsaro bayanan sirri kan yadda za a iya gano masu ba da bayanai ga ‘yan bindiga da abokan huldar su.

Kara karanta wannan

Abinda Shugaba Buhari ke yi kullum don kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

Ya ce gwamnatinsa ta sanya na’urorin daukar hoto na CCTV da za su rika lura da duk wani aiki da motsin jama’a a babban birnin jihar, da nufin bin diddigin maboyar miyagu da munanan ayyukansu.

A cewar sanarwar:

“Gwamna Bello Matawalle ya ce gwamnatinsa za ta bai wa gwamnatin Jamhuriyar Nijar tallafin sabbin motoci guda biyar don samar da aikin sintiri na musamman a Maradi da sauran sassan Jamhuriyar Nijar da ke kan iyaka da jihohin Zamfara, Katsina da Sokoto."

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

"Gwamnan ya ce za a mika motocin ga Gwamnan Jihar Maradi a wani bikin da za a yi daga baya tare da amincewar Shugaba Mohamed Bazoum."

Ya bukaci a yi taro akai-akai kan harkokin tsaro da Ministan Tsaro na Nijar da Gwamnan Maradi da Gwamnan Jihar Zamfara da na Jihohin Katsina da Sokoto domin kawo karshen matsalolin tsaro da kasashen biyu ke fuskanta.

Kara karanta wannan

Zamu share yan bindiga daga doron ƙasa, Shugaba Buhari ya tabbatarwa gwamnan Sokoto

Da yake mayar da martani, Shugaba Bazoum ya gode wa Gwamna Bello Matawalle bisa wannan ziyarar da kuma duk wani kokari da ya yi na kawo karshen matsalolin rashin tsaro da ke addabar kasashen biyu, musamman ma kan iyakar Maradi da Arewa maso Yammacin Najeriya.

Shugaban kasa Mohamed Bazoum ya bukaci Matawalle da ya ci gaba da kokarin da ake yi na magance matsalar rashin tsaro a Zamfara ta hanyar samar da sabbin hanyoyin samar da zaman lafiya da aka riga aka samu a yankin.

Ya kara da cewa gwamnatin Jamhuriyar Nijar a shirye take ta ba da goyon baya a yaki da rashin tsaro.

Shugaba Bazoum ya kuma bukaci gwamnonin Najeriya da su aiwatar da dokar hana shigo da babura baki daya zuwa Najeriya.

Shugaban ya yi nuni da cewa matsalar ‘yan bindiga a fadin jamhuriyar Nijar na zuwa ne daga Madawa da Bayan Dutsi har zuwa Najeriya ta yankin Maradi, amma ya yi fatan da taron da goyon bayan da Gwamna Matawalle ya ba gwamnatin Nijar, lamarin zasu magance matsalar.

Kara karanta wannan

Shugabar Makaranta ta hana dalibai mata 2 zana jarabawa, tace sai sun cire Hijabi

'Yan bindiga sun fito da sabon salo a Zamfara, sun saka sabon haraji

A wani labarin, 'yan bindiga a jihar Zamfara sun fito da sabon salo mai hatsarin gaske yayin da suka bukaci a biya sama da Naira miliyan 1 a matsayin haraji kan yankuna daban-daban a kananan hukumomin Zurmi, Kaura Namoda da Birnin-Magaji na jihar.

Yankunan da abin ya shafa sun hada da Birnin Tsaba, Gabaken Mesa, Gabaken Dan-Maliki, Turawa, Askawa da Yanbuki, jaridar Vanguard ta ruwaito.

Mazauna wadannan yankuna an ce yanzu haka suna cikin karkashin ‘yan bindigar da suka kafa gwamnatinsu a yankunan da lamarin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel