Karin Bayani: Gwamna Masari ya dira gidan kwamishinan da aka kashe, jami'ai sun cafke mutum daya

Karin Bayani: Gwamna Masari ya dira gidan kwamishinan da aka kashe, jami'ai sun cafke mutum daya

  • Gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, ya ziyarci gidan da aka kashe kwamishinan kimiyya da fasaha, Rabe Nasir
  • Rahoto ya bayyana cewa bayan maharan sun kashe shi, sun ja gawarsa zuwa ban ɗaki kuma suka garkame kofar
  • Kwamishinan yan sanda na jihar yace an fito da gawar, kuma jami'ai sun damke mutum ɗaya da ake zargi

Katsina - Yanzu haka gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari, yana gidan kwamishinan da yan bindiga suka hallaka.

Dailytrust ta rahoto yadda aka hallaka kwamishinan kimiyya da fasaha, Dakta Rabe Nasir, a gidansa dake Fatima Shema Estate cikin kwaryar birnin Katsina.

Maharan sun daɓa masa wuka a cikinsa a cikin dakin hutu, sannan suka ja gawarsa zuwa cikin ban ɗaki suka kulle.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: An kashe kwamishina, Rabe Nasir, a gidansa da ke Katsina

Katsina
Yanzu-Yanzu: Gwamna Masari ya dira gidan kwamishinan da aka kashe, ana kokarin kwato gawarsa Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gwamna Masari, manyan jami'an gwamnatin Katsina, da jami'an tsaro yanzu haka suna gidan marigayin a kokarin da ake na zaro gawarsa daga inda aka kulle.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Har zuwa yanzun da muke tattara muku wannan rahoton ana cigaba da kokarin balle kofar ban dakin domin zaro gawarsa.

Manyan jami'an da suka isa wurin

Kwamishinan yan sanda, Sanusi Baba, da shugaban jami'an tsaron farin kaya (DSS) reshen jaihar Katsina duk sun isa gidan yayin da jami'an su ke cigaba da kokarin ɓalle kofa domin ciro gawar.

Hakanan kuma jami'an sun gano wayar salula ta marigayi kwamishina da kuma ta wani mutum ɗaya daban.

Sannan jami'ai sun fitar da manema labarai daga cikin gidan yayin da zasu fara aikin ceto gawar marigayin daga ban ɗaki.

An samu nasara

Daga baya, kwamishinan yan sanda ya bayyana cewa jami'ai sun samu nasarar fito da gawar, kuma an kaita cibiyar kula da lafiya ta gwamnatin tarayya, Katsina.

Kara karanta wannan

Gwamnatin jihar Katsina ta bude layukan sadarwa a kananan hukumomi 17 na jihar

"An daɓa masa wuka tun daren jiya amma bamu sani ba sai yau da yamma. Mun kama wanda ake zargi, kuma zamu cigaba da bincike."

A wani labarin na daban kuma Hukumar NHRC zata binciki mummunan kisan da akai wa Fulani a jihar Edo

Hukumar kare hakkin bil adama ta ƙasa (NHRC) ta sha alwashin gudanar da bincike kan kisan Fulani a jihar Edo.

Sakataren hukumar, Tony Ojukwu, yace lamarin ya munana sosai, kuma duk me hannu a kisan zai girbi abinda ya shuka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel